Biyo bayan sakin shugaban majami’an Methodist a Najeriya da aka sace, shugaban ya bayyana cewa sai da cocin ta biya kudin fansa na kusan kwatan miliyan na dala kafin a sake shi.
Rikicin da aka yi a makon jiya tsakanin masu hakar zinare a arewacin kasar Chadi ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 100, in ji gwamnatin kasar.
Shugaban Cocin Methodist a Najeriya ya samu ‘yancinsa kwana guda bayan wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi garkuwa da shi a kudu maso gabashin kasar, kamar yadda ‘yan sanda suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press da yammacin ranar Litinin.
Shugaban ya bayyana ilimi a matsayin abin da ke samar da ci gaba a kowace ƙasa kuma yana mai cewa gwamnatinsa ta himmatu don ganin ta kara rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta.
Gwamnatin jihar Anambra ta saka dokar Hana fita a wasu kananaan hukumomi 7 dake jihar ta Anambra sakamakon tsanantar kashe kashe a jihar.
Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya fada a ranar Laraba cewa jarirai 11 da aka haifa sun mutu a wata gobara da ta tashi a sashen jarirai na wani asibitin yankin a garin Tivaouane mai tazarar kilomita 120 daga gabashin Dakar babban birnin kasar.
Shugaba Buhari ya bayyana fatansa na ganin cewa a karkashin Sheikh Mohamed kasashen biyu za su ci gaba da ba da himma wajen tabbatar da dorewar tsaro, da karfafa hadin gwiwa wajen yaki da ta'addanci.
Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele bai yanke shawarar tsayawa takarar shugaban kasa a watan Fabrairu mai zuwa ko kuma wani mukami da aka zaba ba kuma zai ci gaba da rike mukaminsa na yanzu.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi bulaguro zuwa birnin Abidjan a Cote d'Ivoire domin halartar taron da Majalisar dinkin duniya da ta shirya dangane da kwararowar hamada.
Dakarun rundunar soji ta yammacin Afirka sun kashe mayakan jihadi kimanin 20 a cikin kwanaki uku a wani samame da suka kai a yankin tafkin Chadi, kamar yadda rundunar hadin gwiwa ta sanar a yau Lahadi.
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira a jiya Lahadi ga hukumomin soja a Burkina Faso, Guinea da Mali su mika mulki ga farar hula cikin gaggawa, ya kuma tunatar da duniya da ta cika alkawuran “yanayi na gaggawa".
Mataimakin kakakin Majalisar Dinkin Duniya, Farhan Haq ya ce babban sakataren ya isa kasar Senegal da yammacin jiya Asabar, zai kuma tafi Nijar a ranar Litinin da kuma Najeriya ranar Talata sannan kuma ya koma New York.
Buhari ya yi wadannan kalamai a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar.
Shugaba Buhari ya ce alhakin asarar rayuka da dukiyoyi dole ya hau kan masu daukar matatar man ta haramtacciyar hanya, “kuma dole ne a kama su a kuma a hukunta su.
Wani Ma’aikacin kamfanin Dangote ya ce a wannan watan matatar man za ta fara aiki a kwata na hudu na shekarar 2022.
Akalla mutane 15 ne aka kashe a hare-haren da aka kai a arewa maso gabashin Najeriya cikin makon nan.
Kungiyar IS ta dauki alhakin fashewar wani bam da ta ce ya kashe ko jikkata mutane 30 a wata kasuwa da ake sayar da barasa a jihar Taraba a Najeriya, lamarin da ke nuni da fadada yankin da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ke kai hare-hare a kasar.
Najeriya dai na fama da matsalar rashin tsaro yayin da wasu gungun 'yan bindiga da ‘yan ta’adda ke kai hare-hare a kan al'ummomi a sassan arewacin kasar.
Wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga, mai suna Nasanda, ya bukaci gwamnatin jihar Zamfara da ta biya shi kudi Naira miliyan 30 saboda kashe matarsa da kawunta da kuma kanwarta ko kuma ya kashe mutum 300 a matsayin ramuwa.
Gwamnatin jihar Legas ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun Chrisland da ke jihar nan take, har sai an kammala gudanar da bincike kan zirgin cin zarafin wata dalibar makarantar a badalance, yayin wata tafiya da suka yi zuwa birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
Domin Kari