Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Taya Yara Murnar Bikin Ranarsu


Yadda Aka Yi Bikin Ranar Yara
Yadda Aka Yi Bikin Ranar Yara

Shugaban ya bayyana ilimi a matsayin abin da ke samar da ci gaba a kowace ƙasa kuma yana mai cewa gwamnatinsa ta himmatu don ganin ta kara rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi murnar zagayowar ranar yara ta bana tare da matasan Najeriya, inda ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tukuru domin ganin kowane yaro ya samu ilimi, wanda hakan zai sa su samu kyakkyawar makoma.

Wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya fitar ta bayyana hakan.

Shugaban ya amince da matsayin ilimi a cikin ci gaban kowace ƙasa kuma ya himmatu don ganin an ƙara raguwar adadin yaran da ba sa zuwa makaranta.

Ya yarda cewa yayin da ilimin yaran Najeriya zai ci gaba da kasancewa kan gaba a wannan gwamnati, sauran batutuwa - kiwon lafiya, kariya daga cutarwa, muggan kwayoyi, kungiyoyin asiri, fataucin yara da cin zarafi - suna samun kulawar da ake bukata daga gwamnati.

Shugaba Buhari ya yi imanin cewa yaran Najeriya sun cancanci kasa mai mai kwanciyar hankali inda za su iya girma, yin abokai, mu'amala da tafiye-tafiye cikin lumana, sannan su zama shugabanni masu nasara a fannoni daban-daban.

"Tare da zuba jari a cikin abubuwan more rayuwa, ci gaban matasa, ilimi, Watsa Labarai da Fasahar Sadarwa, Tattalin Arziki na Dijital, Al'adu da Nishaɗi a cikin shekaru bakwai da suka gabata, na yi imani muna kafa tushe mai ƙarfi don ingantacciyar rayuwa ga al'ummomi masu zuwa a kasar," in ji shi.

XS
SM
MD
LG