Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Da Ake Kyautata Zaton Masu Tsattsauran Ra'ayi Ne Sun Kashe Mutum 9 A Arewa Maso Gabashin Najeriya


Wasu 'yan tawayen masu tsattsauran ra'ayi.
Wasu 'yan tawayen masu tsattsauran ra'ayi.

Akalla mutane 15 ne aka kashe a hare-haren da aka kai a arewa maso gabashin Najeriya cikin makon nan.

Wani hari da ake zargin masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama ne ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tara a yankin arewa maso gabashin Najeriya, kammar yadda 'yan sanda da shaidu suka bayyana a jiya Alhamis.

Wannan na daya daga cikin munanan hare-hare a cikin makon nan a yankin da ke fama da rikice-rikice.

Akalla mutane 15 ne aka kashe a hare-haren da aka kai a arewa maso gabashin Najeriya cikin makon nan.

Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai farmaki garin Geidam da ke kan iyaka a jihar Yobe, inda suka bude wuta kan mazauna garin, kamar yadda shaidu suka bayyana.

Wadanda aka kashen sun hada da mata biyu da wani sifeton ‘yan sanda mai ritaya, in ji Dungus Abdulkareem na rundunar ‘yan sandan jihar Yobe.

‘Yan ta’addan sun zo ne da kafa kuma “sun fara harbi,” wani mazaunin garin Babagana Umar ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press.

"Duk mun dauka sojoji ne ke harbi kafin daga baya muka fara jin mutane suna ihu da gudu," in ji Umar.

"Sun kona wata makaranta kafin su afkawa wani wurin da ake sayar da barasa da shakatawa inda 'yan ta'addan suka harbe wasu sannan suka daure wasu daga baya suka yanke makogwaronsu."

Har yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin na ranar Laraba.

Sai dai kungiyar IS ta dau alhakin fashewar wani bam a jihar Taraba mai makwabtaka da kasar wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida a farkon makon nan.

Kungiyar ta kuma ce mayakanta sun kashe sojoji biyar a wani hari na daban da suka kai a wani sansanin soji da ke garin Marte a jihar Borno duk da cewa rundunar sojin Najeriya ba ta tabbatar da hakan ba.

Jami’an ‘yan sanda sun ce an tsaurara matakan tsaro a yankunan da aka kai hare-haren.

Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a Afirka mai yawan mutane miliyan 206, na ci gaba da fama da tashe-tashen hankula na tsawon shekaru 10 da masu tsatsauran ra'ayin addinin Islama suka yi a yankin arewa maso gabashin kasar da kungiyar Boko Haram da 'ya'yanta ke yi.

Fiye da mutane 35,000 ne suka mutu yayin da miliyoyin mutane suka rasa muhallansu sakamakon tashe tashen hankula, a cewar shirin raya kasashe na Majalisar Dinkin Duniya.

A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya caccaki ‘yan tada kayar bayan da suka haramta karatun boko a sassan arewacin Najeriya inda suke gudanar da ayyukansu.

“Allah shi ne adalci. Ba za ku iya kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, ku yi ihu Allah Akbar (Allah mai girma ne). Ko dai ba ku san cewa Allah ba, ko kuma kawai ko kuma kuna da wauta," in ji Buhari.

~ AP

XS
SM
MD
LG