Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Bai Yanke Shawara Kan Takarar Shugaban Kasa Ba


Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele

Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele bai yanke shawarar tsayawa takarar shugaban kasa a watan Fabrairu mai zuwa ko kuma wani mukami da aka zaba ba kuma zai ci gaba da rike mukaminsa na yanzu.

Kamar yadda ya bayyana a ranar Asabar bayan da masu kushewa suka bukaci da ya yi murabus sakamakon rahotannin burinsa na siyasa.

Bayan da mai magana da yawun jam’iyyar APC mai mulki ya ce a ranar Juma’a Emefiele ya sayi fom din tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar a wannan wata, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: “Ban yanke wannan shawarar ba.

Emefiele ya ce zai ci gaba da rike mukamin gwamnan babban bankin kasar kuma zai fayyace burinsa nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.

Rahotannin neman takarar shugaban kasar Emefiele ya sa canjin Naira ya kai kusan dala 591 a kasuwannin bayan fage a ranar Juma’a, sabanin naira 413 zuwa 417 a kasuwa a wannan shekarar.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sauka daga mulki bayan ya yi wa'adi na shekaru hudu bayan zaben watan Fabrairun 2023. Jam’iyyar APC ta tsayar da zaben fidda gwanin dan takararta na shugaban kasa a ranakun 30 da 31 ga watan Mayu.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da tsohon gwamnan jihar Legas Asiwaju Bola Tinubu ne kan gaba a fafutukar zama dan takara na gaba da zai jagoranci shugabancin kasar.

Ya kamata jam'iyyun siyasa a Najeriya su zabi 'yan takarar shugaban kasa a ranar 3 ga watan Yuni, kamar yadda hukumar zabe ta bayyana, yayin da za a fara yakin neman zaben a hukumance a watan Satumba.

Emefiele dai ya na yin wa’adi na biyu a babban bankin kasar inda ya bi diddigin tsare-tsare na kudin ruwa, ya bullo da tsarin kula da kudaden, sannan ya kaddamar da wani kamfani da zai taimaka wajen gina ababen more rayuwa a Najeriya.

Karfin siyasa a Najeriya dai ya karkata ne a tsakanin jihohin kudu masu arzikin man fetur, wadanda galibinsu Kiristoci ne, da kuma jihohin arewa da suka fi talauci, galibinsu Musulmi. Buhari dan asalin jihar Katsina ne kuma dan takarar jam’iyyar APC na gaba zai fito ne daga kudu.

~ REUTERS

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG