Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

IS Ta Dauki Alhakin Harin Da Ya Hallaka Mutum Uku, Ya Raunata 30 A Jihar Taraba


Wani hari da aka kai a jihar ta Taraba a wani lokaci a baya (Wanna hoto, an yi amfani da shi ne don nuna misali)
Wani hari da aka kai a jihar ta Taraba a wani lokaci a baya (Wanna hoto, an yi amfani da shi ne don nuna misali)

Kungiyar IS ta dauki alhakin fashewar wani bam da ta ce ya kashe ko jikkata mutane 30 a wata kasuwa da ake sayar da barasa a jihar Taraba a Najeriya, lamarin da ke nuni da fadada yankin da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ke kai hare-hare a kasar.

Arewa maso gabashin Najeriya, musamman jihohin Borno da Yobe, sun shafe shekaru goma suna fama da tashe-tashen hankulan masu kishin Islama, amma a baya ba a kai hari a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin yankin Najeriya.

Fashewar ta auku ne a ranar Talata a garin Iware da ke karkara, kuma da farko ‘yan sandan yankin sun ce mutane uku ne suka mutu yayin da 19 suka jikkata. Ba a iya samunsu nan take a ranar Alhamis don yin tsokaci kan ikirarin kungiyar IS ko kuma adadin wadanda suka mutun ba.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar da yammacin ranar Laraba a wata tashar aika sako ta Telegram da kungiyar IS ke amfani da ita wajen yin farfagandarta, kamar yadda Reuters ya ruwaito, kungiyar ta bayyana wadanda suka tayar da bam a kasuwa a matsayin "sojojin khalifanci a tsakiyar Najeriya".

Duk fadin Najeriya, kasa da ke da mafi yawan al'umma a Afirka, na fama da karuwar laifuka da tashe-tashen hankula, wanda ya ta'azzara sakamakon matsin tattalin arziki da annobar COVID-19 ta haifar.

Ana samun yawaitar fashi da makami a ko’ina, sace-sacen mutane domin neman kudin fansa ya zama ruwan dare gama gari, sannan kuma yankin arewa maso yamma ya sha fama da matsalar sace-sacen yara a makarantu da kuma hare-haren wuce gona da iri da wasu gungun ‘yan bindiga suka kai kan garuruwa da kauyuka.

Rikicin mafi muni kuma mafi dadewa, shi ne a yankin arewa maso gabas, inda kungiyoyin kishin Islama da ke gaba da juna na Boko Haram da kungiyar IS a yammacin Afirka (ISWAP) suka yi ta kashe-kashe da sace-sace mai dimbin yawa a yayin da suke fafatawa da sojojin Najeriya.

A harin na baya-bayan nan da aka kai a garin Geidam na jihar Yobe, mayakan Boko Haram sun zo da sanyin safiyar Alhamis inda suka kona wata makaranta da wasu gine-gine masu zaman kansu, kamar yadda mazauna garin biyu da wasu majiyoyin tsaro biyu suka bayyana.

Mazauna garin sun ce an kai hari a wani wurin shan barasa a yankin. Daya ya ce ya ga gawarwaki tara, yayin da daya ya ce ya ga gawawwakin mutane da dama ciki har da mata biyu. Har yanzu hukumomi ba su fitar da adadin wadanda suka mutu ba.

~ REUTERS

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG