Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Da Hadaddiyar Daular Larabawa Za Su Inganta Alakar Tsakaninsu


Buhari da Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan
Buhari da Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan

Shugaba Buhari ya bayyana fatansa na ganin cewa a karkashin Sheikh Mohamed kasashen biyu za su ci gaba da ba da himma wajen tabbatar da dorewar tsaro, da karfafa hadin gwiwa wajen yaki da ta'addanci.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta kara yin aiki tukuru domin ganin an samu ci gaba wajen habaka dangantaka tsakanin Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a cewar wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya fitar a ranar Asabar da Muryar Amurka ta sami kwafin.

A wata ‘yar gajeruwar tattaunawa da Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, sabon Sarkin Abu Dhabi kuma shugaban kasar UAE a wata ziyarar ta’aziyya da ya kai fadar shugaban kasa a jiya Juma’a, shugaba Buhari ya bayyana ta’aziyyarsa da ta Najeriya kan rasuwar marigayi shugaban kasar, Sheikh Khalifah ya kuma taya sabon shugaban kasar murnar zabarsa.

Shugaba Buhari ya bayyana fatansa ta ganin cewa a karkashin Sheikh Mohamed kasashen biyu za su ci gaba da ba da himma wajen tabbatar da dorewar tsaro, da karfafa hadin gwiwar yaki da ta'addanci, da saukaka harkokin kasuwanci da zuba jari, da samar da wadata da ci gaba.

A cikin shekaru bakwai na Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Kasashen biyu sun gudanar da tattaunawa sosai a tsakaninsu da suka kai ga cimma yarjejeniyoyin da dama da kuma yarjejeniyar fahimtar juna da suka share fagen kara yin hadin gwiwa da fahimtar juna da ci gaba da dangantakarsu.

XS
SM
MD
LG