Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Halaka Mutum Uku, Ya Raunata 19 A Jihar Taraba


Fashewar bam a kasuwa
Fashewar bam a kasuwa

Najeriya dai na fama da matsalar rashin tsaro yayin da wasu gungun 'yan bindiga da ‘yan ta’adda ke kai hare-hare a kan al'ummomi a sassan arewacin kasar.

Mutane uku ne suka mutu yayin da 19 suka jikkata bayan fashewar wani abu a wata kasuwa mai cunkoson jama'a a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin kasar, kamar yadda 'yan sandan yankin suka sanar a ranar Laraba.

Najeriya dai na fama da matsalar rashin tsaro yayin da wasu gungun 'yan bindiga da ‘yan ta’adda ke kai hare-hare a kan al'ummomi a sassan arewacin kasar.

Usman Abdullahi, kakakin rundunar ‘yan sandan Taraba, ya ce fashewar ta auku ne a kauyukan Iware a ranar Talata a wurin shan ruwa a wani yanki na wata kasuwa mai cike da cunkoson jama’a, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku tare da jikkata wasu fiye da goma.

Abdullahi ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters ta wani sakon wayar tarho da ya aikewa kamfanin cewa "ana zargin cewa bama-bamai ne suka tashi.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

~ REUTERS

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG