Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutuwar Dinbin Mutane Sanadiyyar Fashewar Matatar Mai a Imo, Bala'i Ne Ga Kasa Baki Daya - Buhari


Fashewar wata haramtacciyar matatar mai
Fashewar wata haramtacciyar matatar mai

Shugaba Buhari ya ce alhakin asarar rayuka da dukiyoyi dole ya hau kan masu daukar matatar man ta haramtacciyar hanya, “kuma dole ne a kama su a kuma a hukunta su.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaron kasar da jami’an tsaro na leken asiri da su kara kaimi wajen dakile ayyukan matatun mai biyo bayan mutuwar gomman mutane da daren Juma’a bayan fashewar wata haramtacciyar matatar mai a dajin Abaezi da ke karamar hukumar Ohaji-Egbema a jihar Imo.

Fashewar matatan mai
Fashewar matatan mai

Da yake mayar da martani ga abin da ya bayyana a matsayin “musiba da bala’i ga kasa baki daya,” Shugaba Buhari ya ce alhakin asarar rayuka da dukiyoyi dole ya hau kan masu daukar matatar man ta haramtacciyar hanya, “kuma dole ne a kama su a kuma a hukunta su.

Buhari ya mai da martanin ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar wacce Muryar Amurka ta sami kwafinta.

Da yake mika sakon ta'aziyya game da lamarin ga iyalan wadanda lamarin ya shafa, al'ummar Ohaji Egbema da ma gwamnati da jama'ar jihar Imo, shugaban ya bukaci shugabannin al'umma, 'yan sanda, da jami’an lekan asiri da kada su sake barin faruwar irin wannan lamarin mai ratsa zuciya a duk fadin kasar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG