"Na sami rahoton da ya firgita ni game da mutuwar jarirai 11 a cikin gobarar da ta faru a sashen ilimin halin ɗan adam na asibitin Mame Abdou Aziz Sy Dabakh da ke Tivaouane," in ji Sall a cikin shafin twita ba tare da yin ƙarin bayani game da gobarar ba.
Sall, wanda ya kai ziyarar aiki a Angola ya kara da cewa, "Ga uwayensu da iyalansu, ina nuna matukar juyayi na."
Ministan lafiya na Senegal Abdoulaye Diouf Sarr, ya fada a gidan talabijin mai zaman kansa na TFM cewa "bisa binciken farko da aka yi, wani dan gajeren zango ne ya yi sanadiyar gobarar."
Sarr, wanda ke birnin Geneva na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce zai katse tafiyar, kuma zai koma Senegal cikin gaggawa.
Demba Diop Sy, magajin garin Tivaouane, daya daga cikin birane masu tsarki na kasar Senegal kuma cibiyar sufuri, ya ce har yanzu 'yan sanda da jami'an kashe gobara na can a asibitin, amma bai bayar da karin bayani ba.