Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SALLAR IDI: Buhari Ya Tabo Batun Tsaro, Ya Bada Tabbatar Ba Da Tallafin Kudi


Shugaba Buhari (Facebook/Bashir Ahmad)
Shugaba Buhari (Facebook/Bashir Ahmad)

Buhari ya yi wadannan kalamai a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar.

Yayin da watan Ramadan ke karatowa, kuma Musulmi ke gudanar da bukukuwan Sallah, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon gaisuwarsa ga Musulman Najeriya da ma duniya baki daya na murnar zagayowar wannan rana.

Buhari ya yi wadannan kalamai ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya fitar wacce Muryar Amurka ta sami kwafinta, inda ya ce:

“Bayan azumi, a bana, muna da dalilin maraba da bukin da bege. Yakin da ake ta yi da ‘yan ta’addar da suke aika aika da sunan Musulunci ya kusa kawo karshe,” inji Shugaban.

Ya cigaba da cewa, “A watan da ya gabata, an kashe shugaban ISWAP a wani hari da aka kai ta sama. Tun daga sabuwar shekara, dubban mayaka sun mika wuya don shiga shirye-shiryen gyara hali. Yankunan da, a da, suka mamaye ana ganin dawowar wadanda aka tilasta wa barin muhallansu. A karshe dai al’amura sun fara komawa daidai a arewa maso gabas. Tsari ne na tsawon lokaci.

“Tare da ayyana kungiyoyin ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, ana fuskantar kalubale daban-daban na ‘yan fashi da garkuwa da mutane a jihohin arewa maso yamma da Arewa ta Tsakiya, inda ake kuma fatattakarsu, aka kuma sayi makamai a baya bayan nan domin dakile ayyukan ta’addanci. .

“Hakazalika, gwamnatin na samun rahotanni masu ban sha’awa na ayyukan musamman na dakile satar danyen mai a yankin Kudu-maso-Kudu, tare da kama dinbin man da aka tace ba bisa ka’ida.

XS
SM
MD
LG