Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta kashe mayakan ISWAP fiye da 70 a arewacin kasar da ke kan iyaka da Nijar, a wani samame da ta kai ta sama.
Gwamnatin Biden ta baiwa Najeriya damar siyan manyan jirage masu saukar ungulu na kai hare-hare na kusan dalar Amurka biliyan 1 duk da damuwar da kasar ke da ita ta zargin take hakkin bil adama yayin da kuma take fama da barazanar kungiyoyin 'yan bindiga da masu tsattsauran ra'ayi a arewacin kasar.
Tun shekarar da ta gabata ne Najeriya ta shirya gudanar da kidayar jama’a a amma aka yi watsi da shi saboda karuwar rashin tsaro.
Shugaba Buhari ya umarci hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa (NIWA) da ta kara kaimi wajen tabbatar da tsaron tafiye-tafiyen koguna a kasar.
Gwamnatin Birtaniya ta kulla yarjejeniya da kasar Rwanda domin aikewa da wasu masu neman mafaka zuwa kasar dake gabashin Afirka, matakin da 'yan siyasa masu adawa da 'yan gudun hijira suka yi Allah wadai da shi.
A ranar Litinin ne Mataimakin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya bayyana cewa zai tsaya takarar shugabancin kasar a shekara mai zuwa, lokacin da Shugaba mai ci, Muhammadu Buhari, zai sauka daga mulki.
A ranar Alhamis ne wani alkalin kotun tarayya ya yanke hukuncin cewa, daga yanzu za a ci gaba da gudanar da dukkan shari’ar ta’addanci a Najeriya ta hanyar amfani da fasahar zamani wato ta amfani da bidiyo da kuma ta kafar sadarwa ta intanet.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya karbi bakuncin sabon zababben shugaban jam’iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu.
Bayan harin da aka kai wa jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna a kwana-kwanan nan, shugaban kwamitin Majalisar Dattijan Najeriya na ganin kamar yadda a ke sa ma ‘yan siyasa ido wajen bin diddigin layukan sadarwansu, ya kamata jami’ai su dinga amfani da layunkan sadarwa wajen gano yan ta’adda.
Kamfanin matatar mai na Dangote mai iya samar da 650,000(bpd) na mai a kowace rana, wanda ake ginawa a Najeriya, zai fara aiki nan da kwata na hudu na shekarar 2022, in ji Babban Darakta rukunin kamfanin, Devakumar Edwin a ranar Lahadi.
Mutane fiye da 90 da ke cikin wani kwale-kwale mai cunkoso sun nitse a tekun Bahar Rum, a wani sabon bala'i da ya shafi bakin haure da su ka taso daga arewacin Afirka don neman ingantacciyar rayuwa a Turai a cewar kungiyar likitocin agaji ta Doctors Without Borders (MSF).
Shugaban ya shawarci attajirai Musulmi da su guji almubazzaranci, yayin da wasu ke fama da yunwa da fatara.
Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindigar da su ka kai hari ne, sun tuntubi wasu iyalai a Najeriya inda suka ce suna tsare da ‘yan uwansu da suka bace sakamakon harin da aka kai kan wani jirgin kasa a wannan makon, kuma za su bukaci a biya su kudin fansa, a cewar iyalan a ranar Alhamis.
A cikin watan Maris, lokacin da Shugaba Joe Biden ya yi sanarwar maraba da 'yan gudun hijirar Ukraine 100,000, inda ya ba da matsayin kariya na wucin gadi ga wasu 30,000 da suke zama a Amurka tare da dakatar da hana korar 'yan kasar Ukraine.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Juma’a a Abuja, ya ce Najeriya a shirye ta ke ta yi maraba da karin kudirori da saka hannun jari kan fasahar lataroni, yayin da ya yaba shirin kafa Cibiyar Raya Afurka ta Microsoft, da za ta ci dala miliyan 200.
Wasu mahara da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun kai hari a wani rukunin gidajen masu karamin karfi da ke Kofar Gayan a karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna inda suka yi garkuwa da mutane shida da suka hada da wani jami’in Kwastam da dansa.
Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, ta musanta bayanai da ake yadawa, wadanda ke nuni da cewa 'yan fashin daji sun tare hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Alhamis din nan.
Yanzu haka an gano gawarwaki takwas, sannan mutum 26 sun jikkata yayin da ake kokarin gano inda sauran fasinjojin suke.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kakkausar suka kan harin da aka kai filin jirgin saman Kaduna da kuma jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna a ranakun 26 da 28 ga watan Maris, wanda rahotanni suka ce an kashe mutane da dama, ko jikkata, ko kuma sace su.
"Kare bakinka daga kiran sunan matata," abin da Smith ya fadi kenan biyo bayan sabanin da ya kai ga mari.
Domin Kari