Wata kotun birnin Bolga Tanga a arewa maso gabashin kasar Ghana ta bada umarnin kama tsohon shugaban karamar hukumar Bawku, Musah Abdulai, a matsayin mutumin da take neman jin ta bakinsa a shari’ar da take yi game da tashin hankali da ke faruwa a yankin.
Kungiyar Editocin Najeriya da Kungiyar Kare Hakkokin Jama’a da Tattalin Arziki sun kai karar Shugaba Muhammadu Buhari da Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Kasa (NBC) kotu kan soke lasisi tare da rufe kafafen labarai 53 a kasar saboda rashin sabunta lasisi.
Wasu ‘yan bindiga da ba tantance ba a jihar Imo, sun halaka wasu sarakuna a jihar tare da awon gaba da wani ba-saraken gargajiya a yankin Orlu da ya sha fama da tashe tashen hankula haka kuma a can jihar Anambra an halaka wani jam'in soji mai mukamin Manjo wanda a halin yanzu ake bincike a kai.
Iyaye da daliban jami’o’in gwamnati da suka shafe watanni shida suna gida sakamakon yajin aikin da kungiyar ta ASUU ke yi, sun bude kunnuwansu domin jin yanda zata kaya a taron da kungiyar malaman da gwamnatin tarayya ke yi a wani wurin da ba a bayyana ba a Abuja.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi ‘yan Najeriya cewa kar su yarda yakin basasan shekaru 1967 zuwa 1970 ya maimaita kansa.
Kocin Senegal Aliou Cisse ya ce wasan kwallon kafa na kasa-da-kasa - da kuma musamman gasar cin kofin kasashen Afirka – ba zai yiwu ya wasa mai martaba na biyu ba ga wasanni kulob kulob a Turai, ya kuma kalubalanci Napoli da ta ce kada a kara sayin ‘yan wasan Afirka.
Shugabannin Musulmi sun gargadi mahalarta wani taron bude masallaci da makaranta a birnin Accra da su kasance masu neman zaman lafiya da hadin kai tsakanin addinai dake makwabtaka da juna a kasashen mu na Afrika ta Yamma da don ci gaban al’ummar mu.
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya fada a birnin Abuja cewa gwamnatinsa ta sakar wa ma’aikatar sojan kasar mara ta yi duk mai dacewa ta kawo karshen rashin tsaro da ya addabi kasar da ya kira da “aikin hauka”.
Napoli ta yanke shawarar ci gaba da rike babban dan wasanta Victor Osimhen akalla na karin shekara guda kuma ba za ta saurari duk wani tayi daga kowace kungiya komin tsokar kudin da zasu taya a wannan bazara ba.
Akalla mutane uku ne suka kone kurmus a daren ranar Litinin bayan da wata babbar tankar mai dauke da man fetur ta fashe da wuta a lokacin da ta samu matsalar birki a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.
A yau Talata wata kotun Tarayya a Abuja ta ki amincewa da bukatar neman beli ga shugaban kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra IPOB, Nnamdi Kanu da ke tsare.
Kasashen Najeriya, Morocco da Tanzania sun yi nasarar samun gurbin wakiltan Afrika a gasar cin kopin duniya na ‘yan mata kasa da shekaru 17 da za a yi a kasar India a cikin watan Oktoba.
Safarar dan Adam da ayyukan masu alaka da ita suna cikin muggan laifuka a kasar Ghana, kuma a dan haka ne aka baiwa rundunar ‘yan sandan kasar horo na musamman a kan yanda zasu tinkari yaki da wannan dabi’a a cikin kasar.
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce tilas ne a dauki matakin kawo karshen asarar rayuka da ya zama ruwan dare a kasar sakamakon hare haren kan mai uwa da wabi da 'yan bindiga ke yi.
Matasa a garin Nkoranza na jihar Bono ta Gabas a kasar Ghana sun kai hari a kan shelkwatar ‘yan sandan yankin inda suka lalata abubuwa suka kuma bukaci a yiwa wani da ake kira Albert Donko mai shekaru 28 da aka kashe shi yayin da yake tsare a hannun ‘yan sanda adalci.
Rundunar sojan Ruwa ta Najeriya, ta sanar cewar ta kama wasu jiragen ruwa goma sha biyu, dake dakon mai da aka sato a yankin Neja Dalta a wani samamen hadin gwiwa da ta kaddamar a yakin mai suna Operation Dakatar da Barawo.
Hukumomin kasar Kamaru sun tabbatar da wata rundunar tsaro ta musamman ta ceto wasu yara daga hannun masu garkuwa da mutanen domin samun kudin fansa bayan wata musayar wuta tsakanin jami’an tsaron a garin Mayo Rey da ya yi sanadiyar raunata mutum guda a cikin masu garkuwan.
Farautar mutumin da ya kai harin kan mai-uwa-da-wabi da safiyar yau Talata a gundumar Brooklyn ta birnin New York ta hadu da tsaiko yau da rana yayin da aka gano kyamarar daukar hoto a tashar jirgin kasa na layin 36th street da ya kamata ta dau hoton maharin ta lalace.
Domin Kari