Sha’anin tsaron yana kara rancabewa a jihar Imo dake kudu maso gabashin Najeriya. Jihar Imo itace ke biye da jihar Anambra wurin yawan tashe tashen hankulan ‘yan bindiga dake kisan gilla ga jama’ar yankin da basu san hawa basu san sauka ba.
Kisan gilla na baya baya nan shine wanda wasu ‘yan bindiga suka aikata, inda suka bindige wasu sarakunan gargajiya su uku a yankin Orlu a jihar tare kuma da awon gaba da wani ba-saraken gargajiya Eze Magnus. Kawo yanzu ba a san inda suka nufa da ba-saraken ba.
A jihare Anambra mai makwabtaka da jihar Imo, nan ma wasu ‘yan bindga sun hallaka wani babban jami’in soji mai mukamin Manjo. Hukumomin tsaro a jihar Anambra sun ce suna gudanar da bincike a wannan batu.
Harkar tsaro a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya na ci gaba da zama babban kalubale, kamar yanda kwamishinan rundunar ‘yan sanda na jihar Imo Muhammad Ahmad Barde ya bayyana wa Muryar Amurka a wata tattaunawa.
Ya ce “yankin Orlu kam, a gaskiya suna da wurin boyo can gefen don akwai wani daji wanda kuma har yanzun nan muna nan muna gudanar da bincike don mu gano inda suke don mu kai musu hari.” Ya kara da cewa ‘yan bindigan sun kashe akalla jami’ansu guda bakwai da ma sojoji da wasu jmi’an tsaro.
Ya ce duk da matsalolin da suka kan fuskanta yayin gudanar da ayyukan su, zai iya cewa abubuwa na zuwa da sauki saboda sun fara samun taimakon kayan aiki. Saboda a cewarsa a kwana kwanan nan ma gwamnan jihar ya sayo musu kayan aiki kuma zasu fara aiki da kayan gadan gadan.
Wani ba-saraken gargajiya a yankin Orlu na jihar Imo, Eze Woha, ya ce kasar Najeriya na fama da rashin tsaro, kama daga batun kabilanci da sauran su. “Ba zaka iya tafiya zuwa inda kake so ba saboda rashin tsaro, don haka muna kira ga gwamnatin Najeriya da ta dubi wannan lamari ta kuma dauki matakan da suka dace,” in ji shi.
Ga dai rahoton Lamido Abubakar Sakkwato daga jihar Imo: