Kalaman na dan shekaru 46 da haifuwan na zuwa ne bayan da shugaban kungiyar Napoli Aurelio de Laurentiis ya ce kungiyar ta kasar Italiya zata daina daukar ‘yan wasa daga Afrika, har sai sun amince da ba zasu yi wasa a gasar cin kofin Afrika da ake yi a duk shekaru biyu ba.
Cisse ya fadawa shirin BBC Sports Africa cewa, dan wasa zai iya yin wasa cikin kungiyoyi 12, amma kungiyar wasa ta kasa kwaya daya kacal.
“Kulob kulob ba za su taba kasancewa sama da tutarmu da kungiyar kasarmu ba. Kuma duk dan Senegal da ke taka leda a Turai, a duk inda yake, idan ya cancanta zan kira shi don ya kare tutar kasar.
"Ina matukar girmama (De Laurentiis) amma ina kalubalantarsa a kan kokarin hana daukar 'yan wasan Afirka."
Lokacin da ake gudanar da gasar cin kofin Afrika - wanda aka saba yi a watan Janairu da Fabrairu shekaru biyu - yana haifar da rashin fahimta tsakanin ‘yan wasa da kungiyoyin Turai na tilasta musu sakin 'yan wasa a tsakiyar kakar wasa.
Napoli ta yi rashin dan wasan baya Kalidou Koulibaly - wanda ya jagoranci Senegal ta samu nasarar lashe gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2021 da aka shirya a bana a Kamaru - da kuma dan wasan tsakiya Andre-Frank Zambo Anguissa don yiwa kasarsa wasa a gasar, yayin da tsaka da kakar bara sannan su biyun ba su buga wasanni shida ba a kungiyar.