Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ba Zata Sake Shiga Yakin Basasa Ba-Shugaba Buhari


Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari (Hoto: Fadar shugaban kasa)
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari (Hoto: Fadar shugaban kasa)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi ‘yan Najeriya cewa kar su yarda yakin basasan shekaru 1967 zuwa 1970 ya maimaita kansa.

Shugaban, wanda ya bayyana son kai a matsayin babban dalilin da ya haddasa yakin basasar da ya lakume rayuka miliyan daya, ya ce ‘yan Najeriya za su ci gaba da zama ‘yan Najeriya dunkulalliyar kasa daya.

Da yake jawabi a fadar gwamnati dake Abuja, yayin da yake karbar bakuncin tsaffin shugabannin jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC), na jihohi, shugaba Buhari ya ce bai kamata a yarda son kai da ya yi sanadin asarar rayukan mutane kusan miliyan daya a tsakanin 1967-1970 ya sake maimaita kansa ba.

Ya kara da cewa, an kafa jam’iyyar CPC a kan ginshikin kishin kasa da biyayya ga hadin kan Najeriya.

Ya ce: “Babban manufarmu ita ce Tarayyar Najeriya. Mu mutane ne. Muna da raunin mu, amma ina tabbatar muku cewa kishin kasa a cikinmu yana da matukar muhimmanci.

“Mun sha fama da matsalolin tun daga ranar 15 ga Janairun 1966 zuwa yau. Kun san abin da nake nufi da wannan; mun kashe junan mu miliyan daya domin mu hada kan kasar nan.

Shugaban ya bukaci daukacin mambobin tsohuwar jam'iyyar CPC da shugabannin siyasa da su kasance masu lura da al'amuran yau da kullum ta hanyar kokarin kiyaye hadin kai, zaman lafiya da amincin al'umma.

Shugaban ya godewa tsaffin shugabannin jam’iyyar da aka hade da ita aka kafa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), bisa yadda a kullum suke bayyana irin nasarorin da gwamnati ta samu, yana mai cewa ko shakka babu za a kara kulawa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG