Garin Bawku, wanda ke zama cibiyar hada hada tsakanin kasashen Ghana da Burkina Faso da kuma Togo, a masa kallon yanki mai muhimmanci ga ‘yan kasuwa a wadannan kasashe.
Amma yakin kabilanci tsakanin kabilar Mamprushi da Kusasi a kan wanda keda ikon mallakar garin Bawku yasa yankin na barazana ga tsaro da zaman lafiyar kasashe musamman a wannan lokaci da Ghana take zuba ido sosai a kan iyakokinta da Burkina Faso wadda take fama da ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda.
A jiya Laraba bakwai ga watan Satumban 2022, kotun mai jagorancin alkalin Justice Alexander Graham ta tsare Ibrahim Mohammed mai lakabi Kwakwa a hannun ‘yan sanda.
An kawo Ibrahim Mohammed wanda ya bude tashar mota ta Asongtaba a birnin Accra kuma shugaban kungiyar matasan kabilar Kusasi a gaban kotu ne bias zarginsa da da mallakar bindiga da kuma harsashai masu rai.
Ya fadawa kotun cewa bindigar da wadannan harsashai da ake batun su, tsohon shugaban karamar hukumar Bawku Musah Abdulai ne ya bashi su.
Kafin dage shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Satumban 2022, Alkalin ya bada umarnin gurfanar da tsohon kantomar Bawku a gaban kotun.
Wannan batu ya taso ne sakamakon tashin hankalin da yaki-ci-yaki-cinyewa a garin na Bawku wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma asarar dukiyoyi masu tarin yawa a yankin dake zama cibiyar hada hada tsakanin Ghana da Burkina Faso da kuma Togo.