Kasashen hudu da suka yi nasarar samun gurbin akwai sababbi biyu a ciki da suka hada da Morocco da Tanzania wadanda suka yi nasarar doke manyan kasashe a wannan gasa da suka hada da Ghana da Kamaru a zagayen kwaf-daya ko knockout a Afrika a wannan mako.
Hukumar CAF ta jinjina wa kasashen, Najeriya da Morocco da kuma Tanzania kana suka musu fatan alheri a India.
Za a fara wasannin cin kofin duniya na ‘yan mata kasa da shekaru 17 ne a ranar 11 zuwa 30 ga watan Oktoban 2022 a Inida. Sai dai babu wata kasar Afrika da ta taba nasarar lashe wannan kofin.
Wannan ne karon farko da Morocco da Tanzania za su shiga wannan gasar daga yankunan Arewaci da Gabashin Afrika zuwa gasar ‘yan ta duniya.
Najeriya dai za ta sake komawa gasar ne bayan ta bayyana sau shida a gasar ta duniya inda ta gaza bayyana a gasar da aka yi a kasar Uruguay a shekarar 2018.
‘Yar wasan Tanzania Clara Luvanga itace tafi yawan zura kwallaye da kwallo 10 a matsakin neman gurbi, lokacin da aka yi wasanni 30 kuma aka zura kwallaye 107
Za a yi gasar ta India ne tsakanin kasashe 16 da za a karkasa su gida hudu.
Za a buga wasannin ne a filaye uku cikin garuruwa daban-daban, da suka hada da filin wasan Kalinga a Bhubaneswar, filin Pandit Jawaharlal Nehru in Margao da kuma filin DY Patil a Navi Mumbai.
A ranar 24 ga wannan watan Yuni ne hukumar FIFA zata gudanar da taron karkasa kasashen da zasu shiga gasar cin kopin duniya ta ‘yan mata kasa da shekaru 17, a helkwatanta a Zurich.