Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Editoci, Kungiyar Kare ‘Yancin Dan Adam Sun Kai Karar Buhari, NBC A Kotu


Kungiyar Editocin Najeriya da Kungiyar Kare Hakkokin Jama’a da Tattalin Arziki sun kai karar Shugaba Muhammadu Buhari da Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Kasa (NBC) kotu kan soke lasisi tare da rufe kafafen labarai 53 a kasar saboda rashin sabunta lasisi.

Wanda ake kuma tuhuma shi ne Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed.

A makon da ya gabata ne dai hukumar NBC ta kwace lasisin gidajen rediyon 53 tare da yin barazanar rufe ayyukansu cikin sa’o’i 24 bisa zargin basussukan Naira biliyan 2.6.

Hukumar da ke kula da ayyukan tashoshin watsa labarai a cikin wata sanarwa a makon da ya gabata ta nemi gidajen rediyon "da su biya duk wasu basussukan kudaden lasisin su kafin ranar 23 ga Agusta, 2022 ko kuma a rufe su daga karfe 12 na tsakar dare a ranar 24 ga Agusta."

Kungiyar editocin ta NGE da SERAP sun kuma nemi kotu ta yi amfani da umarninta na wucin gadi ta hana su rufe ayyuka da kuma kwace lasisin gidajen watsa labarai 53 a kasar, har sai an saurari kara an kuma yanke hukunci kan bukatar da aka gabatar wa kotu a lokaci daya da wannan batu.

A cikin karar, kungiyoyin biyu sun bayar da hujjar cewa, " tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya da yarjejeniyoyin kare hakkin bil'adama kan 'yancin fadin albarkacin baki sun nuna cewa za a iya amfani da wannan 'yancin ta kowace hanya."

NGE da SERAP sun kuma fada cewa, wadannan tanade-tanaden suna nuna cewa kowane mutum na da 'yancin samun dama daidai gwargwado don karba, nema da kuma isar da bayanai ta kowace hanyar sadarwa ba tare da nuna bambanci ba.

“Amfani da dokar NBC da kuma lambar NBC a kan wannan batu ba za a amince da shi ba saboda zai haddasa sabani kana zai tauye ‘yancin fadin albarkacin baki wanda wani bangare ne na zaman lafiyar al’umma da ya kare kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma yarjejeniyoyin ‘yancin dan Adam da Najeriya ke cikin su."

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG