Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Runduna Ta Musamman Ta Cafke Masu Garkuwa Da Mutane A Kamaru


'Yan sanda kwantar da tarzoma a Kamaru.
'Yan sanda kwantar da tarzoma a Kamaru.

Hukumomin kasar Kamaru sun tabbatar da wata rundunar tsaro ta musamman ta ceto wasu yara daga hannun masu garkuwa da mutanen domin samun kudin fansa bayan wata musayar wuta tsakanin jami’an tsaron a garin Mayo Rey da ya yi sanadiyar raunata mutum guda a cikin masu garkuwan.

Wani yunkurin da jami’an tsaro na musamman suka yi a karkashin jagorancin Kanal Dominique Joka ya taimaka wurin cafke wasu masu garkuwa da mutane da suka kwashe wata da watanni suna addabar mazauna yankin Mayo Rey.

Wannan lamari dake zama barazana ga rayukan al’umma ya tilastawa mazauna yankin tanadan shanu da kudade masu dimbin yawa domin yin musaya a duk lokacin da za a yi garkuwa da ‘ya’yan su. Bayan sace yara bakwai, masu garkuwan sun kutsa cikin gandun dajin Benue domin boye su.

Bayan bincike da bayanai da jami’ai suka tattara, an tabbatar da cewa miyagun na cikin gandun dajin Benue.

Kanal Dominique Joka ya kara da cewa "mun samu labarin suna cikin dajin ne shi yasa muka shiga ciki domin kubutar da yaran. Ya ce yayin da masu garkuwan suka ankara mun shigo dajin sai suka bude wuta a kan yaran, ya kuma ce duk wanda zai aikata laifi a yankin mu sai ya dandani kudarsa."

Wani da ya taba fadawa a hannun masu garkuwa da mutanen a watan Faburairu da ya shige ya ce maharan na cin zarafin wadanda su ka kama domin matsawa makiyaya hanzarta kawo kudi da kuma shanu .

Bayan an ceto wadannan yara gwamnan jihar Adamawa ya yi tsokacin yana cewa “Wadannan da aka cafke tsakanin jihar Adamawa da ta Arewa, da muka samu labari ne muka tura jami’an tsaro na musamman wadanda suka yi hobbasa don ganin sun ceto wadannan yara.”

Gwamnan ya tabbatar da cewa an jikata daya a cikin miyagun da aka kama sakamakon wata musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro na musamman.

Ga rahoton Mohamadou Rabiou daga Adamawa a Kamaru:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

XS
SM
MD
LG