Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Sakarwa Sojojinmu Mara Su Kawo Karshen ‘Yan Ta’adda - Buhari


Shugaba Buhari (Instagram/Muhammadu Buhari)
Shugaba Buhari (Instagram/Muhammadu Buhari)

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya fada a birnin Abuja cewa gwamnatinsa ta sakar wa ma’aikatar sojan kasar mara ta yi duk mai dacewa ta kawo karshen rashin tsaro da ya addabi kasar da ya kira da “aikin hauka”.

A cewar wata sanarwar da babban hadimin shugaban kasa a kan harkokin kafafen labarai, Mallam Garba Shehu, shugaban Buhari yana mai da martani ne a kan hare hare na bayannan a jihohin Kaduna, Filato da kuma Sokoto.

Sanarwar da aka yiwa take, ‘Shugaba Buhari na Allah wadai da hare haren Kaduna, Filato da Sokoto, ta jajantawa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu.

Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan sun sace akalla mutanen 50 a Damari, karamar hukumar Birnin-Gwari a jihar Kaduna, a ranar Litinin, kana suka kora daruruwan mazauna yanki suka bar unguwannin.

A jihar Filato kuma, an kashe mutane goma sha takwas bayan da ‘yan bindiga da ‘yan sa kai suka yi arangama a karamar hukumar Wase a jihar Filato a ranar Litinin.

Da yake mai da martini ga wadannan hare hare a ranar Talata, shugaban ya ce “Muna baiwa rundunar tsaron mu cikakken dama su murkushe kuma su kawo karshen wannan hauka.”

A cewar Shehu, shugaban kasa ya sake duban lamarin biyo bayan rahotanni a kan asarar rayuka da dama da aka samu a wadannan hare hare kana ya sha alwashin bada dukkan gudunmuwa daga gwamnatin tarayya ga jihohi.

“Ina Allah wadai da wadannan hare haren rashin imani a kan kasar. Ina kuma kara tabbatarwa jihohi taimakon gwamnatin tarayya. Ina mika ta’aziya ga iyalan mutane da suka mutu. Wadanda suka ji rauni Allah basu lafiya cikin gaggawa,” inji shugaban kasa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG