Runudnar sojan ruwa ta kasa ta yi shelar cewa jami’anta dake yaki da satar danyen mai a yankin Niger Delta mai arzikin mai ta samu nasarar kamawa tare da kwace wani jirgin ruwa na kwale-kwale dake dauke da danyen mai da aka sato a yankin.
Rundunar ta ce ta samu wannan nasara ce bisa kaddamar da wani sabon shiri da ta fito da shi a baya bayan nan mai suna “Dakatar da Barawo.”
Darektan yada labarai na rundunar sojan ruwa ta kasa Commodor Ayo Adedetun, ya ce rundunar ta kaddamar da wani shiri na musamman dake yakar masu satar danyen mai na yankin Niger Delta tare da hadin gwiwar babban kamfanin mai na kasa (NNPC), kuma sun yi nasarar kama wani danyen mai da aka sato.
Adedetun ya kara da cewa, shirin da aka kaddamar a farkon watan Afrilun wannan shekara ya samu nasarori da dama na kama barayin danyen mai a Niger Delta, haka zalika suka kama kananan jirage guda tara dauke da danyen mai da aka sato daga yankin Bille.
Darektan yada labaran rundunar sojan ruwa ta kasa ya ci gaba da cewa, jami’an su sun kama tataccen mai da aka sato daga yankin tsibirin Boni dake jihar Rivers, haka ma a jihar Bayelsa an kama wani mai na gas da aka sato a birnin Yanobuwa a cikin motocin dakon mai bayan an tace man ta bayan fage.
Babban kalubalen da rundunar sojan ruwa ke fuskanta shine rashin samun hadin kan al’ummomin yankin da matasa da kuma kungiyoyin sa kai wurin gudanar da ayyukan rundunar na tinkarar masu satar danyen mai, a cewar Adedetun.
Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto daga Port Harcourt: