Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Ghana Sun Kara Azama A Yaki Da Safarar Dan Adam


IGP and senior police officers of Ghana
IGP and senior police officers of Ghana

Safarar dan Adam da ayyukan masu alaka da ita suna cikin muggan laifuka a kasar Ghana, kuma a dan haka ne aka baiwa rundunar ‘yan sandan kasar horo na musamman a kan yanda zasu tinkari yaki da wannan dabi’a a cikin kasar.

Ma’aikatar ‘yan sandan Ghana tare da hadin gwiwar hukumar shari’a ta kasa da kasa (International Justice Mission) ta ilmantar da manyan jami’an ‘yan sandan kasar da basu kwarewar da suke bukata wurin dakile wannan mugun aiki.

Manyan ‘yan sanda daga jihohin Ashanti, jihar Tsakiya da ta Yammacin Ghana aka basu wannan horo da dabarun gudanar da bincike da kama mai lafin da wanda ake kokarin safararsa da kuma dabarun kwace kayan aikin haramtacciyar ciniki.

Darektan kungiyar International Justice Mission na kasa a Ghana, Will Lathrop ya yi imanin cewa wannan horo da aka ba wa jami’an tsaron zai yi tasiri wurin dakile laifukan safarar bil Adama.

“Muna sa ran zasu kammala daukar wannan horo su fito da kwarewa da zasu yi aikin hadin gwiwa ko kuma su samu kwarewar kula da wandanda ka yi yunkurin safarar su,” in ji shi.

Ya kuma jaddada muhimmancin igantaccen mu’amala domin kulla yarda da mutanen da abin ya shafa da kuma masu ruwa da tsaki.

Kungiyar ta International Justice Mission (IJM), itace kungiyar kasa da kasa mai kare mutane dake cikin talauci da ake cin zarafin su. IJM tana da kawaye na hukumomin kasashe da suke gudanar da shirye shirye 24 a kasashe 4 domin yaki da safarar dan Adam da cin zarafin mata da yara da kuma wuce gona da iri da ‘yan sanda ke yi a kan talakawa.

Wasu daga cikin mahalartan sun bayyana farin cikin su tare da kyautata zato wannan horo ya sabonta dabaru da kwarewar su na aiki.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG