A Nuwamban bara, Kungiyar ta EEA ta bada sanarwar cewa mutane dubu biyu da talatin da takwas ne suka mutu da kananan shekaru a shekara ta 2020 a Tarayyar Turai da ya hada da kasar Iceland, Leichtenstein, Norway, Switzerland da Turkiyya.
A wata sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan kasar Olumuyiwa Adejobi ya fitar a jiya, ya ce Sufeto Janar Alkali ya bada umarnin tawagar binciken ta yi aiki tare da INEC domin gaggauta daukar mataki a game da bayanan da wasikar ta kunsa.
Yayin da sauran kasashen duniya suka yi nisa da kwashe 'yan kasashensu daga Sudan mai fama da tashin hankali, Najeriya ta ce yau ko gobe za ta fara jigiliar 'yan Najeriya mazauna Sudan wadanda suka fara kokawa da irin tsaka mai wuyar da suke ciki.
Yaran da suka rasa iyayensu a rikicin boko haram, a gabashin arewacin Najeriya da wasu daga Sokoto sun kwashe shekaru biyar suna samun kulawa a dukkannin bangarorin rayuwa, daga neman ilimi daga matakin firamare har zuwa jami'a da kuma bangaren koyon sana'o'in hannu.
A lokacin gaisuwar idin karamar sallah da al’ummar Abuja da a ka canka karkashin ministan Abuja Muhammad Musa Bello zuwa fadar Aso Rock, shugaban ya nemi ahuwar jama’a a kusan shekaru 8 da ya yi ya na mulkin kasar.
Shugabannin cocin katolika sun yi Allah wadai da yadda kisan gilla ke dada ta'azara a kasar, tare kuma da yin kira ga gwamnati ta kara tsaro da bincike, domin kare mutane da hukunta masu wannan aika aika.
Gwamnatin Najeriya tayi alkawarin bada goyon baya domin kaddamar da haddadiyar Kasuwar sufurin Afirka ta Sama (SAATM) Single African Air Transport Market. Lamarin da zai taimaka wajen bunkasa hada-hadar jiragen sama a Afirka.
Jami’an ‘yan sanda sashin binciken manyan laifuka da na leken asiri reshen Alagbon a Lagas sun kama wani mai sana’ar POS a jihar Kwara bisa zargin kashe naira miliyan dari biyu da tamanin (280) da mutane suka tura mishi bisa kuskure.
Kungiyar kwallon kafar Barcelona ta kasar Spain ta maida martani kan binciken da ake yi kan ta, bisa tuhumar biyan alkalan wasa don ba su nasara, tana mai bayyana zargin a zaman farmaki kawai na adawa.
Wani sabani da ya shiga tsakanin Shugaban kasar Sudan na Soji Abdul Fattah Durham da shugaban dakarun 'yan tawayen RSF Muhammad Hamdan Dagalo bayan kin amincewar Durham da yarjejeniyyar zaman sulhun na shirin mika mulkin kasar ga farar hula domin dawo da kasar a tafarkin demokradiyya.
Majalisar Darektocin Jam'iyar PDP sun ja hankalin Hukumar Zaben Najeriya ta kiyaye sauya sakamakon zaben jihar Adamawa bayan riga-mallam massalacin da wani jami'in Hukumar zabe ya yi
Hukumar zaben Najeriya INEC ta dakatar da shugaban hukumar na jihar Adamawa daga shiga ofishin ko kusantar ofishin har sai an dauki mataki na gaba.
Ma’aikatan tashar jiragen saman Najeriya sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyu daga yau Litinin bayan cikar wa'adin sanarwar kwanaki 14 da suka yiwa Ministan Sufurin Najeriya ya sh.
Kungiyoyin raya kasa sun yi taro domin tabbbatar da zaman lafiya a Najeriya, tabbatar da zaman lafiya da hadin kan 'yan Najeriya bisa la'akari da irin kalaman da wasu 'yan siyasa da basu ji dadin yadda sakamakon zabe ya kasance ba.
Da akwai yiwuwar cewa bayanai na baya-bayan nan a game da tsohon karamin Ministan man Najeriya Timipre Sylva mai murabus su iya sanya kafar ungulu a takarar sa na gwamnan jihar Bayelsa bisa zargin ya yi amfani da takardun shaidar karatu na boge.
‘Yan adawa a Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijer sun bayyana damuwa dangane da yadda bangaren rinjaye ke haddasa cikas ga tsarin sulhun dake tsakanin bangarorin siyasar kasar.
Babban bankin Najeriya ya ce yana ci gaba da buga sababbin takarkun kudi, sai dai har yanzu 'yan Najeriya na kokowa da cewa, suna cigaba da fuskantar matala wajen samun takadun kudin.
Gwamnatin kasar ta Birtaniyya ta sanar da wannan matakin ne a cikin wani sako da ta wallafa a shfinta na yanar gizo cikin kundin tsarin aikin lafiya da masu ayyukan jinkai.
Domin Kari