Masu gabatar da kara sun zargi Barcelonar da biyan kudi sama da fam miliyan 7, ga Jose Maria Enriquez, tsohon mataimakin babban kwamitin alkalan wasa.
To sai dai Shugaban kungiyar ta Barcelona, Joan Laporta ya musanta cewa an biya kudin ne don sayen nasara a wasanni, yana mai cewa an ba da kudaden ne saboda wani aiki na shawarwarin kwararru.
A watan jiya wata kotu ta sami kungiyar da laifi a tuhumar da aka yi mata na cin hanci da rashawa, cin amana, da kuma ba da bayanan kasuwanci na karya.
Hukumar kwallon kafar Turai ta UEFA, ta ce ita ma tana nan tana gudanar da binciken kan lamarin.
Ana tsallen murna a kungiyar Napoli ta kasar Italiya, sakamakon dawowar shahararren dan wasan gaban ta Victor Osimhen, gabanin fafata wasa ta 2 ta matakin QF ta gasar zakarun turai.
A makon jiya ne aka buga wasan farko tsakanin Napoli din da AC Milan, inda Osimhen bai sami bugawa ba sakamakon rauni da ya ji, wasan da kuma ya karkare AC Milan ta yi galaba kan Mapoli da ci 1-0.
Tauraron matashin dan wasan na Najeriya na haskawa sosai a kungiyar wacce kawo yanzu ya zura mata kwallaye 25 a cikin wasanni 30 a wannan kakar wasannin.
Mai horar da ‘yan wasan kungiyar ya tabbatar da dawowar ta Osimhen a bakin daga a yau Litinin, inda kuma yace hakan ya karawa daukacin ‘yan wasan kungiyar kwarin gwiwa, kuma a shirye suke su tare kwallon da Milan ke bin ta bashi.
Yanzu haka gasar Premier ta bana ta kara rincabewa, ba’a san maci tuwo ba sai miya ta kare, biyo bayan kunnen doki da Arsenal ta yi da West Ham United da ci 2-2 a jiya Lahadi.
Arsenal wadda ke bukace da lashe gasar ta bana karon farko a cikin shekaru kusan 20, Yanzu haka ita ce ke saman teburin gasar da maki 74 a cikin wasanni 31, tare da tazarar maki 4 tsakanin ta da Manchester City mai bin ta da maki 70 a cikin wasanni 30, wato kenan, tana da sauran bashin wasa daya da zata buga ta daidaice da Arsenal.
Idan City ta yi nasara a wasan da take da bashin ta, maki daya ne kacal zai bambance tsakaninsu. Karawar da za su yi a ranar 26 ga wannan watan na Afrilu, ita ce ake hasashen za ta bambance tsakanin aya da tsakuwa a bana.
Arsenal dai ta dade tana jagorancin teburin gasar ta Premier, tare da bayyana kudurinta na cewa wannan karon, tana son ta kawo karshen kamfar kofin gasar ta Premier.
Manchester City da Yanzu haka ke rike da kofin, ta kwararo ta, kuma kunnen doki biyu da Arsenal din ta yi a baya-bayan nan, ya sa City na neman kamo ta.
Anya Arsenal na iya lashe gasar ta bana kuwa, ko kuwa Manchester City za ta yi mata jakar Baya?
Muna dakon jin amsoshi da ra’ayoyin ku, a shafukan mu na yanar gizo, a voahausa.com ko kuma SASHEN HAUSA.COM, ko a shafukanmu na FACEBOOK, INSTAGRAM da TWITTER.
Sai mun ji daga gare ku!