Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali, ya bada umarnin kaddamar da bincike idan ta kama da kuma hukunta kwamishanan zabe na Jihar Adamawa Hudu Yunusa Ari.
Wannan Lamarin ya biyo bayan samun wata wasikar da Hukumar Zaben Najeriya INEC ta rubuta mai dauke da kwanan wata 18 ga watan Afirilu inda tayi bayani dala-dala a game da rashin da’ar da ake zargin Ari da aikatawa.
Sufeto Janar Alkali ya yi wa tawagarsa ‘yan sanda masu bincike su yi aiki tare da INEC wajen bincike da kuma hukunta ri.
A wata sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan kasar Olumuyiwa Adejobi ya fitar a jiya, ya ce Sufeto Janar Alkali ya bada umarnin tawagar binciken tayi aiki tare da INEC domin gaggauta daukan mataki a game da bayanan da wasikar ta kunsa.
Da yake bayani a game da jajircewar ‘yan sanda wajen tabbatar da demokradiyya, Shugaban ‘yan Sandan ya tabbatar wa ‘yan Najeriya da a’ummar kasashen duniya cewa, hukumar ‘yan sanda ba za ta daga wa kowa kafa ba wajen bankado musabbabin wannan rashin da’ar da kwamishanan zaben ya aikata tare da tabbatar da an hukunta duk wadanda aka Ambato sunansu a yayin binciken.
Lauyoyi sun yi kira ga kungiyar Lauyoyin Najeriya NBA da su hukunta Ari bisa laifin da ya aikata. Kwararrun lauyoyin karkashin kungiyar JUSTICE HOSE INTERNATIONAL JHIO sun yi kirar ne cikin wata wasika da suka aike wa shugaban kungiyar lauyoyin Najeriyan Yakubu Maikyau a Abuja. Darektan gangamin, Toyo Jimmy wanda ya rattaba hannu akan wasikar mai kwanan wata 20 ga watan Afirilu.