Wasu daga cikin yara marayun da suka rasa iyayensu a rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya suna cikin gata na samun rayuwa ingantacciya sanadiyyar wani bawan Allah da ake kira Alhaji Alhaji Ummarun kwabo AA wanda ya assassa wata makaranta a sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya da zummar bai wa wadannan yara kulawar da ta dace.
Yaran da adadinsu ya haura 160 gami da wasu marayun daga jihar sokoto sun kwashe shekaru biyar suna samun kulawa a dukkanin bangarorin rayuwa, kama daga neman ilimi, koyon sana'o'i da kowane irin gata da yara masu iyaye raye suke samu koma fiye da hakan.
Wannan shine ya kasance makasudin da yasa wasu daga cikin magadan yaran sukanyi tattaki daga jihohin Borno da Yobe zuwa Sokoto a kowace shekara domin ganin yadda yaran suke rayuwa, suke cike da gamsuwa da abinda sukan gani na irin kulawar da yaran suke samu kamar yadda wani mai suna Musa Ari daga jihar Yobe ya sanar da wakilin Muryar Amurka Muhammad Nasir Sokoto cewa, duk da cewa a can inda suka fito ma ana daukar nauyin marayun, to sai dai ya ce akwai banbanci da irin kulawar da suke samu a nan Sokoto inda ake daukar nauyin karatun yaran tun daga matakin Firamari har zuwa jami'a.
Kazalika ita ma shugabar kungiyar iyayen yara marayu ta jihar Borno, haj. Fatima Yahay Kolo ta sanar da wakilin na Muryar Amurka cewa, suna so su ma yaran su zama masu kwazo domin su zama masu taimaka wa wasu. Inda ta kara da cewa, akwai wani yaron da suke hira da shi sai yace idan ya girma ya zama kaman baba jarma (sunan da suke kiran wanda assasa makarantar), shima zai fara daukan marayu daga Sokoto.
Ko da yake a kwai wasu da suke daukan nauyin kula da wasu marayu a yankin na gabashin Najeriya, bisa la'akari da yawan addadin wadanda basu samu irin wannan damar ba, shi wanda ya assasa wannan makarantar ta Jarma UK Academy dake Sokoto, ya ce zasu zauna da su mallaman da suka dauko wadannan daliban, a sake komawa Maiduguri da Yobe, a sake debo marayu mata da maza daga 200 abun da yayi kasa. ya kuma kara da cewa zasu cigaba da gudanar da wannan aikin da suke gudanarwa.
Babu shakka kula da rayukan marayu, abu ne da ake sa ran zai amfanar da su kansu marayun da ma al'ummar da suke zaune a cikinta. Dalilin da yasa jama'ar jihohin Borno da Yobe bayan damuwar da suke da ita akan makomar marayun da ba su samu gata ba a lokaci daya suke cike da gamsuwa da yadda marayu na yankunan nasu, suke cigaba da samun gata a jihar Sokoto. A hirarsa da wakilin Muryar Amurka, Baba Gana Aji, shugaban kungiyar Borno Muslim Forum daga Maiduguri, yace waddanan yaran dai Allah ya basu gata, yace an tsamo su kuma alhamdulillahi baza a kwatantasu da wadanda suke can gida ba kuma sai dai mucewa yaran su kara himma kuma su fitar da mu daga kunya; mutum ya dau nauyinka zai baka komai da komai, ai sai ka zauna kayi ta karatu. Ya kuma kara da cewa suna fata cewa a cikinyaran za a samu injiniyoyi, likitoci da dai kwararu a fannonin rayuwa daban-daban.
Yanzu haka dai hukumomi da kungiyoyi da ma daidaikun mutane masu hali ne suke ta fafutukar kula da rayukan marayu ta yadda zasu amfanar da kansu da ma al'ummar da suke rayuwa a cikin ta.
A saurari cikaken rahoton Muhammad Nasiru Sokoto: