Ana ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun shugaban Sudan da na mataimakinsa a Khartoum.
Rashin mutumta wannan yarjejeniyya da Durham yayi ya sanya mataimakinsa Muhammad Hamdan Dagallo kuma shugaban ‘yan tawayen Rapid Response Forces RSF wanda aka fi sani da JANJAWEED ya sha alwashin ganin bayan Durham a cewar Mahmood Hausawiya wani mazauni garin Kassala a yankin gabashin Sudan.
A tattaunawarsa ta wayar tarho da Aisha mu’azu a shalkwatar Muryar Amurka a Washington DC, Mahmood yace wani da ya sani ya kira shi ta wayar tarho kana ya sanar da shi irin halin da al’ummar kasar mazauna Khartoum suka tsinci kansu da sanyin safiyar yau Litinin, bayan da karar bindigar da ke tasowa daga musayyar wutar da dakarun suke yi ya tsananta, lamarin da ya tilasta musu sulalewa zuwa wasu garuruwa dake kusa da babban birnin kasar gudun kada yi rikicin ya rutsa da su.
Tun bayan da dakarun SAf da na RSF suka hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar el-Bashir a shekara ta 2019, dakarun RSF ne suke tsare mahimman waurare a kasar, ciki har ha sasanin dakarun sojin kasar wanda ya kasance karkashin ikon su da rikici ya kaure tsakanin bangarorin, sai dai daga bisani dakarun sojin Sudan karkashin ikon shugaba Abdul-Fattah sun dawo da sassanin karkashin ikon su daga bisani kuma aka cigaba da gwabza fada daga wajen sansannin sojojin.