Dalilan da suka haifar da wannan yajin aiki na gargadi da ma’aikatan sukeyi sun hada da rashin bayyana sabotsarin aikin su wanda akayi tun shekaru bakwai da suka gabata da kuma batun rushe ofishin su dake Laagos.Ma’aikatan sun fra yajin a bisa dalilin rashin tabbatar da sabon tsarin aikinsu da kamfanonin jirage 4 suka yi tun shekaru 7 da suka gabata.
Ma’aikatan sun sanya shinge akan hanyar shiga cikin filin jirgin ta barin matafiya cikin gida a tashar jirgin Murtala Muhammad dake Lagas, matakin da ya dakatar da dukkanin harkoki a tashar.
Tun farko dai ma’aikatan sun bada sanarwar shiga yajin aikin kwanaki 2 a jiya Lahadi.
Wannan mataki ya sanya damuwa a zukatan kamfanonin jiragen, musamman na bangaren yadda zai shafi hada-hadar harkokin fasinjoji lamarin da ya sa wasu cikin su suka fara tuntunbar shugabannin kungiyoyin ma’aikatan domin kawo karshen sabanin.
Tun a makon da ya gabata, kungiyoyin ma’aikatan suka sanar da mambobinsu a game da shirin da suke yi na shiga yajin aiki na gargadi tsakanin ranar yau Litinin da gobe Talata na 2023 sannan idan har ba a biya musu bukatunsu ba, zasu zarce har sai baba ta gani.
Kungiyoyin ma’aikatan jiragen sama biyar ne suka shiga yajin aikin; kuma sun hada da NUATE kungiyar ma’aikatan sifirin jiragen sama ta kasa, sannan akwai kungiyar manyan ma’aikatan harkokin zurga-zurgar jirage ta Najeriya (ATSSSAN), kungiyar Najeriya na kwararun ma’aikatan zurga-zurgar jiragen sama ANAP da kuma kungiyar matuka jiragen sama da injiniyoyi na Najeriya da kuma gamayyar kungiyar ma’aikatan gwamnati da ma’aikatan nishadi ta kasa.
Ma’aikatan sun ce tun farko sun baiwa Ministan sufurin Najeriya sanarwar kwanaki 14 a ranar 7 ga watan Fabrairu na wannan shekara amma ba a dauki wani mataki ba har sai da wa’adin da suka bashi ya shude.
Kungiyoyin ma’aikatan suna korafi a game da rashin aiwatar da karin albashin da aka musu da kuma lisafin da ya hau bayan da aka yi wa albashin hukumar NIMET kwaskwarima tun daga shekara ta 2019 da kuma kin amincewa da fitar da sabon tsarin aikinsu da hukumar albashi na kasa (NSIWC) da kuma ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya (OHCSF) suka ki yi.
Ma'aikatan sufurin jiragen sama sun kaddamar da zanga-zanga a birnin Lagas inda rahotani suke bayyana cewa, hukumomin tsaro sun kama wani dan jarida mai daukan hoto bisa dalilin cewa, ya hallarci zanga-zangar dan gudanar da aiki shi.