Da yake jawabi a wajen bude babban taron Bishop-Bishop karo na 48 a birnin Yaoundé, shugaban kungiyar Episcopal na Kamaru (CENC), Bishop Andrew Nkea ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi a cikin ‘yan watannin da suka gabata a kasar. Babban Bishop na Bamenda da takwarorinsa sun sake tabbatar da tsarki da mutunta rayuwar dan Adam.
Babban Bishop din ya bayyana irin alhinin da suka shiga bayan wadannan kashe-kashen da aka yi a Kamaru lamarin da ya ce ya rutsa da wani dan jarida Martinez Zogo a Yaoundé da kuma wani iyali mutane shida da aka sheka su har lahira, sannan ya bukaci al'umma baki daya su mutumta rayuwar dan Adam wanda ya ce, Baiwa ce daga Allah tun daga lokacin da aka haife shi har ya zuwa karshenta.
Bishop Andrew Nkea ya tunatar cewa kashe mutum zunubi ne da ya saba wa doka ta 5 ta shela, wadda ta bayyana karara cewa “Kada ka yi kisa”.
Wannan kiran ya zo ne a yayinda kashe kashe ya yi yawa a Kamaru. An yi mafi ban mamaki a Nanga-Eboko (Jihar Center), inda aka kashe mutane shida dangi daya a ranar 5 ga Afrilu. CENC na fatan za a gano ainihin wadanda suka kashe wadannan ‘yan kasar tare da hukunta su.
Duk da wannan hali da ake ciki, akwai alamar bege inji shugaban katolikan Kamaru. “Alhamdu lillahi, kwanciyar hankali na dawowa a jihohin Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma. An sake bude wasu masana’antu kuma yara da dama na komawa makaranta. Wannan babbar alama ce ta bege, amma ya kamata a kara kaimi kan tsaro , acewar shi.
Duk da barazanar da kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ke yi a yankin Arewa mai nisa da kuma rikicin Anglophone, Bishop Andrew Nkea ya tabbatar da cewa Cocin Katolika zata cigaba da yin addu'a da kokarin samar da zaman lafiya a Kamaru.