Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai POS Ya Shiga Hannun Jami’ai Bayan Handame Naira Miliyan 280


A person holds the new naira notes after the government releases it to then public.
A person holds the new naira notes after the government releases it to then public.

Jami’an ‘yan sanda sashin binciken manyan laifuka da na leken asiri reshen Alagbon a Lagas sun kama wani mai sana’ar POS a jihar Kwara bisa zargin kashe naira miliyan dari biyu da tamanin (280) da mutane suka tura mishi bisa kuskure.

Bayanai na nuni da cewa, Alfa Rafiu, mai POS din ya dauki makonni yana kashe kudade da aka yi ta tura mashi cikin kuskure. Banda alkhairi da yayi da kudin, ya sayi motoci da gidaje sannan ya biya wa mutane kujerar Ummara

Daga bisani, Yan sandan sun kama mutumin a maboyarsa dake yankin Abayomi a yammacin karamar hukumar Illori.

Bisa ga bayanin 'yan sanda, an turawa wanda ake zargin kudaden cikin asusun ajiyarsa na banki cikin kuskure ’yan makonni da suka gabata ne, kuma maimakon ya tuntubi bankunan da suka tura mishi kudin, sai ya shiga wadaka da kudi.

Rahotanni sun nuna cewa a lokaci daya, Rafi’u ya koma attajiri inda ya sayi gidaje da motoci, sannan ya biya wa wasu mutane kudin kujerar Ummara, lamarin da ya sanya al’umar da yake zaune cikinsu mamakin yadda a lokaci guda Rafiu ya kudance alhalin basu san shi da wata sana’ar da ta wuce ta P.O.S ba duk ko da cewa ya yiwa mutane da dama alkhairi.

Bayan da suka ankara, bankunan da suka yi kuskuren tura kudi a cikin asusun ajiyar wanda ake zargi, suka yanke shawarar kai rahoto wajen ‘yan sanda sashin manyan laifuka da masu bincike dake Lagas, wanda ya sanya ‘yan sanda suka yi aiki da bayanan da suka samu da ya kai ga Rafiu shiga hannu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kwara Ajayi Okasami ya tabbatar da aukuwar lamarin.

XS
SM
MD
LG