Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gurbatacciyar Iska Ta Na Haddasa Mutuwar Yara 1,200 A Kowace Shekara


Wildfires-Retardant Pollution
Wildfires-Retardant Pollution

A Nuwamban bara, Kungiyar ta EEA ta bada sanarwar cewa mutane dubu biyu da talatin da takwas ne suka mutu da kananan shekaru a shekara ta 2020 a Tarayyar Turai da ya hada da kasar Iceland, Leichtenstein, Norway, Switzerland da Turkiyya.

Ya zuwa yanzu, gurbatacciyar iska ce ke sanadin mutuwar yara masu kananun shekarun da suka gaza 18 a duk fadin Turai; lamarin da yake haifar da ta’azzarar hadarin kamuwa da manyan cuttutuka can gaba a rayuwarsu , a cewar hukumar harkokin yanayi na Tarayyar Turai a yau Litinin.

Duk da irin cigaban da aka samu, yawan sinadaren dake gurbata muhalli a yawancin kasashen Turai ya zuwa yanzu ya yi kazamin zarta wanda ma’aunin da Kungiyar Lafiya Ta Duniya ta amince da shi musamman ma a kasashen da suke tsakiyar gabashin Turai da kuma Kasar Italiya, a cewar Kungiyar ta Tarayyar Turai EEA cikin wani binciken da suka gudanar sama a kasashen duniya 30 ciki har da mambobin tarayyar kungiyar Turai 27

Rahoton bai kunshi manyan kasashe masu masana’antu ba wadanda suka hada da Rusha, Ukraine da Burtaniya, lamarin da ya ke nuni da cewa alkaluman wadanda suka mutu a zahiri ya zarta wannan adadi.

A Nuwamban bara, Kungiyar ta EEA ta bada sanarwar cewa mutane dubu biyu da talatin da takwas ne suka mutu tun a kananan shekaru a shekara ta 2020 a Tarayyar Turai da ya hada da kasar Iceland, Leichtenstein, Norway, Switzerland da Turkiyya.

XS
SM
MD
LG