Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Za Ta Fara Kwaso 'Yan Kasar Da Ke Makale A Sudan


Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama (Facebook/ Ma'aikatar harkokin hajen Najeriya)
Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama (Facebook/ Ma'aikatar harkokin hajen Najeriya)

Yayin da sauran kasashen duniya suka yi nisa da kwashe 'yan kasashensu daga Sudan mai fama da tashin hankali, Najeriya ta ce yau ko gobe za ta fara jigiliar 'yan Najeriya mazauna Sudan wadanda suka fara kokawa da irin tsaka mai wuyar da suke ciki.

Ministan Harkokin wajen Najeriya Mr. Jeoferry Onyeama ya bada tabbacin cewa daga yau zuwa gobe Najeriya zata fara kwaso 'yan kasarta daga Sudan inda rikicin cikin gida ke ci gaba da kara tsananta. Ministan ya ce suna jiran sahalewar gwamnatin Sudan ne da nufin fara kai 'yan Najeriya zuwa makwabciya, kasar Masar, daga inda za a yi jigilar su domin dawo da su gida Najariya. Ya kuma kara da cewa, tuni aka fara tattaunawa da ofisoshin jakadancin Najeirya da ke Masar da Sudan domin tsara yadda za a yi jigilar . A daidai lokacin da Amurka ta yi amfani da jiragen yaki domin kwashe jami'an difflomassiyarta sama da dari daga birnin Khartoum su ma kasashe irin su Faransa, Jamus da dai sauran kasashe, tuni suka yi nisa wurin kwashe mutanensu dake kasar ta Sudan.

People gather to get bread in Khartoum North
People gather to get bread in Khartoum North

A wani bangaren kuma, a daidai lokacin da ake wannan dogon turanci, dalibai 'yan Najeriya dake birnin Khartoum, sun shaida wa wakilin muryar Amurka Hassan Maina Kaina cewa a halin yanzu suna cikin halin tsaka mai wuya.

Shugaban kungiyar daliban Najeriya na Sudan, Abubakar Babangida mai karatu a jami'ar Sudan International bangaren kiwon lafiya, aji na karshe, ya shaida wa wakilin namu cewa a halin da suke ciki dai a yanzu, dalibai suna cikin fargaba da kuma neman mafita saboda yanayin da suke ciki.

Sannan matsalar da suke fama da ita har da cewa inda daliban suke da kuma gidajen kwanansu, a nan ne ake barin wutar, nan ne ainihin inda ake rigimar kuma nan ne 'yan Najeriya suka fi yawa. Ya kara da cewa, akwai wani sansani inda su bangaren RSF suke, dakarun sojin Sudan suna kawo musu farmaki daga sama da kasa, su kuma suna kokarin kare kansu saboda ana so a amshe wannan sansanin, sannan kuma yaranmu suna makwabtaka da wannan sansannin, to ana ganin cewa tun farko ma dabara ce suka yi suka kafa wannan sansanin a wannan wurin inda gidajen daliban jami'ar Afirka ta kasa da kasa kasancewar akwai 'yan kasashe da yawa a wannan makarantar.

Drone video shows smoke rising over Sudanese city near Khartoum
Drone video shows smoke rising over Sudanese city near Khartoum

k

In this photo provided by Maheen S , smoke fills the sky in Khartoum, Sudan, near Doha International Hospital on April 21, 2023.
In this photo provided by Maheen S , smoke fills the sky in Khartoum, Sudan, near Doha International Hospital on April 21, 2023.

Shugaban kungiyar daliban, ya ce gwamnatin Najeriya ta fa sani cewar, idan cikin kwanaki biyun nan suka wuce basu kwaso su ba, to komai zai iya faruwa.

A hirarsa da wakilin Muryar Amurka a game da makara wajen kwaso 'yan Kasarta da Najeriya, Farfesa Muhammad Tukur Baba, wani kwararre a Najeriya ya bayyana cewa ana iya cewa gazawa ce daga gwamnatin Najeriya da bata yi gaggawar kwaso 'yan kasar da suke Sudan ba kamar rashin wadatattun kayyakin aiki kamar kasashe kamar su Amurka, Faransa da sauransu ba amma ya kamata muyi la'akari cewa, Najeriya bata da irin kayyayakin aikin da suke da shi.

Idan za ayi la'akari da cewa Amurka ta tura sojojin yaki ne cikin dare sannan ta yi amfani da sansaninta na soja da ke Djibouti kafin suka shiga suka dauko 'yan kasarsu. Kuma yana iya yiwuwa duk mayakan sun san cewa idan suka kuskura suka fuskanci Amurka dukansu ba za su ji ta dadi ba kuma, sunyi amfani da iliminsu da kayyayakin aikinsu da suka je da jirage masu tashin ungulu na yaki ba mu da wadannan jiragen da zasu shiga su fito.

Su kansu sojojin Amurka, sai da su ka yi yawon mil dari 800 zuwa su shiga su fita kuma sun yi shi ne cikin dare kuma gaskiya Amurka da Faransa sune masu makamai kowa yasan zata iya musu barna abunda ya kamata muyi.

Smoke is seen in Khartoum, Sudan, Saturday, April 22, 2023. The fighting in the capital between the Sudanese Army and Rapid Support Forces resumed after an internationally brokered cease-fire failed.
Smoke is seen in Khartoum, Sudan, Saturday, April 22, 2023. The fighting in the capital between the Sudanese Army and Rapid Support Forces resumed after an internationally brokered cease-fire failed.

A saurari rahoton Hassan Maina Kaina:

Najeriya Zata Fara Kwaso 'Yan Kasarta Daga Sudan .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:36 0:00

XS
SM
MD
LG