Kwankwaso Yayi Magana Akan Cibok

Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

Gwamnan Jihar Kano Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso ya karbi bakoncin maza da mata masu neman Shugaban Kasa ya dauki matakin nemo dalibai mata da aka sace su sama da 200 a makarantar Sakarandaren Cibok dake Jihar Borno.
Biyo bayan zanga-zangar lumana da gabatar da wasikar korafi daga mata wadanda ke karkashin inuwar gamayyar kungiyoyin sa kai, dana fararen hula, musamman masu fafutukar kare hakkin bil adama dake Kano, wadanda suka kunshi mata da maza, game da halin ko-in-kula da gwamnatin Najeriya ta nuna bayan sace yara dalibai mata su sama da 200 a garin Cibok, gwamnan Jihar Kano, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso yayi magana.

Wakilin Muryar Amurka, Mahmoud Ibrahim Kwari ya ji ta bakin gwamnan game da wannan sakon wasika da masu zanga-zanga suka kai mishi.

“Yau in Allah Ya yarda, wannan takarda zata bar nan ofishin, akan hanyarta na zuwa Abuja. Kuma muna rokon shugaban kasa idan ya samu wannan takarda, ya duba wannan shawarwari, ko koke na wadannan bayin Allah, da suka rubuta,” inji gwamna Kwankwaso.

Mr. Kwankwaso ya cigaba da cewa “anan nake so in godewa wadannan ‘Civil Society Forum na Jihar Kano’ saboda dattakunsu da sanin ya kamata. Basu biyo titi ta yanda mutane marasa mutunci zasu shiga ciki, su jawo wadansu matsaloli akan matsalolin da muke dasu a kasa.

Your browser doesn’t support HTML5

Zanga-Zanga A Kano Saboda Cibok - 3'46"