Hotuna Daga Sassan Duniya Daban Daban

Tsohon mukarabin shugaban Faranasa Emmanuel Macron kan tsaro a gabban yan majalisa gabbanin saurar karar da aka shigar a kansa.

Ma'aikantan kamfanin Amazon a gaban offisin su a yankin San Fernando de Henares yayin da suke gangamin ganin an kara musu albashi saboda yanayin ayyukan su a birnin Madrid dake kasar Spain.

Ashraf Zaki (2nd-L), shugaban yan fim din kasar Masar tare da wasu jaruman fina finan suke raka gawar shahararren dan wasan kwaikwayo Gamil Rateb 

Daraktan Tsara Manufofin Ma'aikatar harkokin wajen Amurka  Brian Hook ya ke gaisawa da  shugabn kungiyar Iran Action Group

Shugaban Amurka Donald Trump yake rabawa mutane abinci a lokacin da ya kai ziyara Chocin darkar Baptist yayin da yake zagaye domin nazarin aiyukan farfadowa daga barnar da mahaukaciyar guguwar  teku Florence  ta yi a garin New Bern, jihar North Carolina, 

Sakataren gwamnatin kasar Kasar Kenya Henry Rotich  yake ajiyewa yan takardun kasafin kudi  domin su karanta

Ma'aikatan Kamfanin Dilancin Labarun  Kasa China, XINHUA ke aikin wallafa zane zanen yan siyasa a birnin Beijing

Hotuna daga sassan duniya dabam dabam kan abubuwan dake faruwa a wasu kasashe.