Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yankewa Bill Cosby Hukunci Bisa Laifin Cin Zarafi Da Aka Sameshi Da Shi


 Bill Cosby
Bill Cosby

Wani alkali a jihar Pennsylvania ya yankewa Bill Cosby hukumcin daurin shekaru uku zuwa goma a gidan yari jiya Talata sabili da bugarwa da kuma cin zarafin wata mace a gidansa cikin shekara ta dubu biyu da hudu. Alkali Steven O’Neill ya kuma bada umarnin a daure Cosby ba tare da bata lokaci ba, tare da watsi da bukatar da aka gabatar ta bada belin Cosby.

Dan wasan barkwancin da mutuncinsa ya zube, ya kasance fitaccen dan wasa na farko da aka samu da laifi tunda aka fara gangamin nan da aka ba lakabi #MeToo da ya sa fitattun mutane suka rasa mukamansu a fannoni da suka hada da kafofin wasannin shakatawa, da siyasa, da kuma sadarwa, sabili da aikata ba daidai ba. Matar Cosby Camille bata kotun a lokacin da aka yake hukumcin.

Alkalin ya bayyana Cosby a matsayin mutum mai cin zarafin mata karfi da yaji. Wannan na nufin za a bukaci Cosby ya rika kai kansa gaban hukuma kowacce kwata, kuma za a sa sunansa a rajistar masu cin zarafin mutane da za a aikawa makwabtansa da makarantu da kuma wadanda yaci zarafinsu. Tilasne kuma ya rika zaunawa da kwararru da zasu rika bashi shawarwari iya tsawon rayuwarsa.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG