Kama daga Numan,Girei,Demsa,Guyuk, Lamurde kai harma zuwa Mayo-Belwa a kullum,batun guda ne-kan tashe tashen hankula dake da nasaba da rikicin Manoma da Makiyaya,lamarin dakan jawo asarar rayuka da kuma dukiya.
Kuma don gano bakin zaren magance wannan matsalar ne ma yasa rundunan yan sandan jihar Adamawa shirya taron masu ruwa da tsaki da ya samu halartar shugabanin tsaro,Sarakuna, manoma da kuma makiyaya.
Abdullahi Ibrahim,dake zama kwamishinan yan sandan jihar Adamawan,yace wanzar da zaman lafiya, ba wai kawai na jami’an tsaro bane,a’a kowa akwai rawar da zai taka.
Masana irinsu Fada Maurice Koiranga na kungiyar kai dauki ta EPRT,na ganin suma kungiyoyi masu zaman kansu akwai rawar da zasu taka domin gano bakin zaren magance tashe tashen hankulan.
To ko me shugabanin bangarorin biyu na manoma da makiyaya zasu ce kan wannan taro da rundunan yan sandan ta shirya? Saurari Rahoton Ibrahim Abdulaziz domin karin bayani
Facebook Forum