Kwararru kan noma na kungiyar ECOWAS sun ce nau’in shanun da makiyaya masu yawo ke kiwatawa ba su dace da killacewa a gidan gona ba, abinda ya nuna wajibcin bullo da dabarar kiwo na killacewa da masu bin damuna.
Dr. Sani Abdu daga jamhuriyar Niger, jami’i ne a daya daga cikin kungiyoyin na ECOWAS mai taken “ROPPA” ya faiyace manufofin da ya dace kasashen su dauka kamar dawo da burtali ko kafa sabon burtali da makiyaya masu yawo za su rika bi. A cewarsa abun dake kawo rigima shine makiyayi na cikin kasarsu sai wasu su taso su ce wurin kiwon mallakin kakanninsu ne saboda haka su fice.
"Wani lokacin kuma wasu sai su yi gonaki cikin burtali. A cikin jiharsa, makiyayi babu inda zai tsaya ya yi kiwo sai ya fita waje". Saboda haka inji Dr Abdu, ya kamata gwamnatoci su fito su ba makiyaya hakkinsu. A kebe wuraren kiwo daban da na noma. Da zarar gwamantoci sun yi hakan za'a samu zaman lafiya.
Wani kwararre kan noma da kiwo, Alhaji Abubakar Bappa ya ce wasu makiyayan ba da gangan su ke aukawa fitina da manoma ba, kuma zaman su a daji ya zama nan ne ya dace gwamnati ta shiga can wajen sama mu su lamuran more rayuwa. Ya kuma ce, idan aka lura ba karamin taimakawa makiyaya su ke yiwa tattalin arzikin kasa ba. Albarkacin makiyaya ya sa naman shanu bai fi karfin kowa ba a kasar yanzu a cewar Alhaji Bappa.
Yayin da lokacin girbi ke karatowa, a kan samu kalubale tsakanin manoma da makiyaya, inda makiyayan ke neman sauya zango zuwa inda za su tafi don jiran wata damunar da su ke kira “Mashekari."
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Facebook Forum