Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Kano Na Kwadayin Kafa Dokar Hana Sakin Aure Kamar Yadda Indiya Tayi


A cikin wannan mako ne hukumomi a kasar India suka ayyana wata doka datayi tanadin daurin shekaru uku a kurkuku ga duk magidancin daya yiwa matar sa saki uku a jere lokaci guda a wani mataki na rage sakin aure barkatai a fadin kasa.

Yanzu haka dai mata da Malamai a jihar Kano dake Najeriya na ci gaba da tsokaci dangane da wannan mataki na mahukunta a kasar India, inda suke cewa ina ma za a iya kafa irin wannan doka a jihar.

Kimanin shekaru 2 baya, mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi Na biyu ya kafa wani kwamitin malamai da masana dokoki, shari’a da zamantakewar aure, wadda aka dorawa alhakin Nazarin fitar da wani daftarin doka da zai takaita yanayin sakin aure a sassan jihar Kano, kwatankwacin matakan da hukumomin India suka dauka a kwanan nan.

A cewar Hajiya Altine Abdullahi, duk da yunkurin gwamnatin jihar Kano na daukar nauyin hidimar auren zawarawa a ‘yan shekarun da suka shude, har yanzu alkaluman zawarawa na karuwa a jihar, don haka ne ya kamata a dauki mataki.

Ga Mahmoud Ibrahim Kwari da cikakken rahoto akan hakan...

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG