Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Yace Zarge Zargen Da Ake Yiwa Kavanaugh Siyasace Kawai


Shugaba Donald Trump na Amurka ya sake bayyana cikkaken goyon bayansa ga mutumen da ya bada sunansa don a nada shi a matsayin daya daga cikin alkalan kotun kolin Amurka duk da wani sabon zargin muzgunawa da wata mace ta biyu ta fito tana yi mishi.

Da yake jaddada goyon bayansa a birnin New York inda ya je don halartar babban taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya na shugabannin kasashen duniya da aka bude yau, Trump yace zargin da ake wa Brett Kavanaugh “duk siyasa ce kawai tsantsarta.”

Mujallar New Yorker ce ta fito da rahoton cewa wasu ‘yan Majalisar Dattawa biyu na Amurka sun fara gudanarda bincike kan zargin da wata mace ta biyu mai suna Deborah Ramirez, ‘yar shekaru 35, ta yi na cewa Kavanaugh ya tsaya gabanta tsirara lokacinda suke dalibbai a Jami’ar Yale a shekarun karatu na 1983 zuwa 1984.

Wannan zargin na zuwa ne a daidai lokacinda ake jiran bayyanar macce ta farko, Christine Blasey Ford, a gaban Majalisar Dattawa a ranar Alhamis mai zuwa don bada karin haske ga zargin da tayi na cewa Kavanaugh ya ci zarafinta a lokacinda suke matasa a makarantarsu ta sakandare a shekarar 1982.

Kavanaugh dai ya musanta duka zarge-zargen da matan ke yi mishi.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG