Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Liberia Anyi Zanga Zangar Kan Layar Zanar Da Dala Milyan 100 Suka Yi.


Wani Dan Liberia Yayin Zanga Zangar
Wani Dan Liberia Yayin Zanga Zangar

Daruruwan masu zanga-zanga sun yi maci a Monrovia, babban birnin kasar Liberia don matsa ma gwamnati ta yi bayanin yadda aka karkatar da miliyoyin daloli daga babban bankin kasar.

"Wannan kudin na kasarmu ne, na 'ya'yanmu ne, saboda gobe," a cewar wata daga cikin masu zanga-zangar mai suna Precious Williams 'yar shekaru 43, a hirarta da kamfanin dillancin labarai na Reuters a birnin Monrovia. Ta kara da cewa, "Mun zo nan ne don mu kwato kudinmu."

Takardun kudin Liberia kwatankwacin dalar Amurka miliyan 100 ne Babban bankin na Liberia ya sa aka buga daga kasar waje, to amma nan da nan kudin ya bace bayan da ya iso wasu tasoshin jirgin ruwa biyu na kasar, a tsakanin watan Nuwamban 2017 da watan Agustan 2018, a cewar Ministan yada labarai, Eugene Nagbe a makon jiya.

Wannan adadin kashi 5% ne na daukacin dukiyar wannan kasa ta Yammacin Afirka.

Abun fallasar yanzu ya hana gwamnatin shuga George Weah sakat. Amma a jawabin da ya yiwa al'mar kasar ranar Jumma'a, yayi alkawarin cewa, gwamnati zata hukunta duk wanda aka samu yana da hanu a wannan badakalar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG