Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitocin Soji Da 'Yan Agaji Sun Kai Dauki Jihar Neja


Kakakin Hekwatar sojojin saman Najeriya Air Commander Ibikiunle Daramola, yayi bayani cewa wani bangare na tsarin mulkin Najeriya ya dora musu alhakin samar da dauki ga fararen hula idan bukatar hakan ta taso.

Akan haka ne baban hafsan rundunar sojhin saman Najeriya ya tura tawagar likitocin soja da sauran jami'an kiwon lafiya zuwa jihar Neja domin taimakawa wadanda ambaliyar ruwa ta afkawa gidajen su. A jiya ne suka isa sansanin dake Zungeru da sauran yankunan dake karamar hukumar Wushishi.

Likitocin zasu gudanar da tiyata, tare da duba lafiyar ido da kuma raba maganin tsutsar ciki ga yara da gidan sauro, kuma zasu kai kwanaki biyar suna gudanar da wannan aiki.

Ga Hassan Maina Kaina da rahoto...

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG