Sojojin Myanmar sun kaddamar da shiryayyen kisan kiyashi da kuma ta'addanci kan Musulmin Rohingya, a cewar Ma'aikatar harkokin wajen Amurka, wadda kadan ya rage ta ayyana hakan a matsayin kisan kare dangi ko kuma mummunan laifi kan bil'adama.
Masu bincike sun yi magana da 'yan Rohingya maza da mata wajen 1,000 wadanda su ka gudu zuwa Bangladesh.
Su ka ce sojojin Burma sun harbe tare da karkashe yara kanana, da mutanen da ba su ma dauke da makamai, su ka yi ta jejjefa gawarwakin cikin kabari guda. Daga cikin wadanda abin ya shafa akwai wadanda aka kona su da rai.
Mata sun bayar da rahoton fadawa hannun gungun sojoji masu fyade.
Tun farko wani rahoton MDD ya ce matakan da sojojin na Burma suka dauka da niyyar yin "kisan kare dangi," domin haka majalisar ta bukaci a hukunta wasu manyan kwamandojin kasar.
Facebook Forum