Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Barkewar Cutar Kolera A Nijar


Cutar kolera ta kara bulla a kauyen Dogarawa dake cikin Gundumar Malbaza a cikin jahar Tahoa, inda yanzu haka mutane 20 ke can killace a babban asibitin Galmi.

Wannan annobar ta kolera da ta bayyana a Dogarawa ta biyo bayan wadanda suka bulla a wadansu wurare a cikin jahar Maradi da Birni N'Konni.

Shugaban gundumar Malbaza ya baiwa al'ummar gundumar bayanin bullar cutar inda yace mutane su san da akwai cutar domin su kiyaye, ya kara da cewa an samu sauki domin wadatar kayan aiki da suka samu. Ya bayyana cewa hasarar rayukan da akayi, ya auku ne kafin aka gano cutar. Sun kuma yi kira da gargadi ga al'umma domin su kiyaye da ka'idodin tsafta domin a hana yaduwar kolera.

Ga rahoton Haruna Mammane Bako....

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG