An gudanar da taron shekara-shekara na al’umar Musulman Afirka na nahiyar Turai a kasar Jamus, manyan baki a taron sun hada da Sheikh Aminu Daurawa da Farfesa Mansur Isah Yelwa.
An harbi dan takarar jam'iyyar Republican kuma tsohon shugaban Amurka Donald Trump a wani taron yakin neman zabe a garin Butler da ke jihar Pennsylvania a Amurka ranar Asabar.
Shugaban Amurka Joe Biden da tsohon shugaban kasar Donald Trump sun amince da gudanar da mahawara 2 gabanin babban zaben kasar dake tafe a watan Nuwamba mai zuwa. Ku bibiyi muhawarar kai tsaye a shafinmu na yanar gizo www.voahausa.com
Rundunar yan sanda ta jihar Kano tace ta kama wani matashin daya cinna wuta a wani masallaci yayin da masu ibada ke sallar asuba yau Laraba a garin Larabar Abasawa na karamar hukumar Gezawa.Kimanin mutane 35 al'amarin ya shafa kuma suna karbar magani a Asibitin kwararru na Murtala dake birnin Kano.
Rahotannin dake fitowa daga fadar gwamnatin jihar Kaduna sun yi nuni da cewa an sako gomman dalibai da aka sace daga garin Kuriga na jihar Kaduna.
Bikin, wanda aka fi sani da Nowroz, ya gudana ne a birnin Bonn. Ana bikin sabuwar shekarar a kasashen Afghanistan da Iran da wasu yankunan Turkiya da Iraki.
Mambobin Kungiyar Kwadago ta Najeriya wato NLC sun gudanar da zanga-zanga a fadin kasar sakamakon matsin rayuwa, yunwa da tabarbarewar tattalin arziki a kasar. A wani bangare kuma wasu ‘yan Najeriya sun fito zanga-zangar nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu
Da sanyin safiyar yau Litinin, 19 ga watan Fabrairu ne darurruwan mutane maza da mata suka yi zanga zanga dauke da kwalaye masu rubutu iri iri suna kokawa game da tsadar rayuwa a kasar.
Hukumar Kare hakkin masu sayan kaya ta kasa (FCCPC), ta rufe katafaren kantin Sahad Store, wani shahararren babban kanti a unguwar Garki dake birnin Abuja. An dai zargi hukumar gudanarwar katafaren kantin da karin kudi akan wanda ke rubuce akan kayayyakin dake kan kanta.
An kebe duk ranar 15 ga watan Janairu don tunawa da mazan jiya.
Domin Kari