Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Izala ta Koka Akan Yadda Ake Zubar da Jini


Shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau.
Shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Ganin yadda aka cigaba da yawan kashe-kashe cikin 'yan kwanakin nan kungiyar Izala ta koka da tabarbarewar tsaro a kasar Najeriya

Kungiyar Izala ta koka game da yadda ake zubar da jini a Najeriya musaman a arewacin kasar.

Kungiyar tace hakika kashe-kashe a Najeriya yayi yawa. Akwai tabarbarewar tsaro. Akwai nuna gazawa daga shugabanni. Da arewa tana zaune lafiya domin da shugabanci ake gyara komi.

Mai wa'azi na iya wa'azi da Kur'ani jama'a su ki janzawa amma shugaba na iya cewa a gyara kaza kuma ko domin karfi suna iya gyarawa. Halin tabarbarewar tsaro da Najeriya ta shiga ya damu kungiyar ta Izala. Tun da gwamnatin tarayya ta kasa shin wai kowa ya tashi ya kare kansa ke nan? Idan an shiga irin wannan halin to abun bakin ciki ne. Kuma abun bakin ciki ne ace an kama yara mata da suke karatu a garin Cibok sama da dari amma har yanzu ba'a san inda suke ba.

Daga wata guda kawo yanzu an hallaka rayuka da dama. Domin haka kungiyar ta fahimci cewa akwai wani makirci musamman idan aka dauki kalmar tsohon shugaban kasar Obasanjo da yayi. Kafin wannan lokacin yace akwai shirrin kashe-kashe da zub da jini da za'a yi a kasar. Kafin yayi wanna furucin ba'a kashe kowa a jihar Katsina ba. Ba'a kashe kowa a jihar Zamfara ba. Ba'a kashe kowa a jihar Adamawa ko Taraba ba. Ba'a kuma kashe kowane malami ba. Bayan furucin Obasanjo aka soma ganin kashe-kashe.

Abubuawn dake faruwa yanzu sun nuna furucin Obasanjo gaskiya ne. Ana kokarin a hada Fulani da Hausawa fada. Shiri ne na musamman domin a karya tattalin arzikin arewa. Yanzu an hada fada tsakanin kabilar Tiv da Fulani. Yanzu idan abu ya faru sai ace Fulani ne suka kawo hari. An tashi daga Boko Haram domin ta rikide ta zama wata hanya ta kashe wanda ake son a kashe. Sabili da haka kungiyar Izala bata yadda da abubuwan dake faruwa ba.

Ga rahoto.
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:29 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG