A kokarin dakile rashin tsaro a Abuja mahukuntan Najeriya sun dawo da shingayen sojoji a duk hanyoyin shiga ko fita daga birnin. Matakin dai bai yiwa 'yan majalisar kasar dadi ba domin a cewarsu mutane na shan wahala matuka kafin su kai wuraren aikinsu ko kuma gidajensu.
Sanata Solomon Ewuga yace damuwarsa ta farko shi ne yadda Najeriya take yanzu, ta zama abun tsoro. Kowa na jin tsoron kowa domin baka san wanda yake rike da makami ba. Yace abu na biyu lamarin da ya faru a Abuja ya kawo damuwa kwarai fiye da yadda ake zato. Misali idan mutum ya fito daga Nasarawa da ka kawo Karu to babu tabbacin lokacin da zaka isa cikin Abuja. Yace sojoji sun kafa shinge. Yace shi kansa yayi sa'o'i hudu da rabi tsakanin Karu da Nyanya abun da da minti ashirin zai kai ka. Yace idan aka cigaba da samun jerin motoci haka to abun da ka iya tasowa zai fi abun da ya riga ya faru.
Sanata Ibrahim Kabiru Gaya ya amince da bayanan Sanata Solomon Ewuga amma ya bayar da shawarar yadda za'a samu mafita. Yace wannan shingen da jami'an tsaro suka yi ya sa mutane cikin damuwa. Yace yau kullum ka tashi da safe baka san yadda rayuwar zata kasance ba. An sa mutane cikin halin tsoro. Kana tafiya kana waiwayen bayanka. Yace kullum maimakon a yi gyara sai kara jefa mutane cikin wahala. Yace hanya mai layi biyar an mayarda ita layi daya. Abun da yakamata a yi da sai a sa sojoji biyar, wato soja daya akan kowane layi. Idan soja ya ga wanda bai yadda dashi ba sai ya tsayarda shi. Yace kuma idan an duba daga karshe ba wani abu su keyi ba. Wani zibin ma su karbi wani abu a hannun mutum. Wannan karawa al'umma dake cikin zafi ne da wahala. Ana cikin talauci kuma an sake kara masu wani talaucin. Yace yanzu tafiyar minti talatin sai ka yi sa'o'i uku ko fiye ma. Sai a ga motoci dari uku suna layi. Su ma motocin bamabamai ne. Takurawar tayi yawa. Gwamnatin tarayya lallai ta dauki matakin saukakawa jama'a.
Saidai a wata takarda dake dauke da sa hannun mai magana da yawun sojoji Chris Olu Kolade ya ba jama'a hakuri game da shingayen da aka sa. Yace matsalolin da jama'a ke fama dasu yanzu na wani dan lokaci ne kafin a samu mafita na dindindin.
Ga rahoton Medina Dauda.