Taron da gwamnoni zai duba maganar tabarbarewar tsaro da ya addabi kasar musamman arewa maso gabas da wa'adin dokar ta baci da aka kakabawa jihohin Adamawa, Borno da Yobe ya kare tun ranar 19 ga wannan watan. Bayanai na danganta matsalolin tsaro a kasar da siyasa.
Kungiyar matasan jam'iyyar APC ta arewa maso gabas, yankin da ya fi fama da matsalar tsaro, ta bakin sakatarenta Hashimu Nuhu Hashimu Mailambu, ta roki taron ya samarma matasa aikin yi akan matakin farko da yakamata a dauka domin warware matsalar tsaro. Yace abun da suke nema shi ne a ba matasa aiki a kuma yiwa mutane adalci a shugabanci. Su yi kokari yadda mutane zasu soma yadda da shugabanninsu. Amma idan an ce za'a cigaba da kuntatawa juna to kullum mutane zasu shiga jeji suna shirin fada.
Dangane da bukatar da aka ce hafsoshin sojoji sun bayar na cewa a dakatarda gwamnonin nan uku da jihohinsu suke cikin dokar ta baci, Mailambu yace masu sanya kayan sarki suna taka doka kuma suna bada shawarar da suka ga dama wadanda basu dace ba. Yace a matsayinsu na matasa basu goyi bayan bukatarsu ba. A bar masu gwamnoninsu su cika alkawuran da suka yi masu.
Kundun tsarin mulkin Najeriya bai ba shugaban kasa ba ikon tsige wadanda aka zaba. Yace ba gaskiya ba ne sojoji su ce gwamnonin na yi masu katsalandan a harkokin tsaro.
Ga rahoton Sa'adatu Fawu.