Wani mazaunin unguwar Garki Sani Tela, ya gayawa Sashen Hausa na Muriyar Amurka cewa mutumin yana tambayar mutane inda masallacin Izala take a unguwar, da suka lura da take takensa suka gane cewa, akwai alamun bashi da kyakkawar niyya a zuciya.
Da yake magana kan wannan al'amari babban sakataren kungiyar Jama'atul Nasril Islam Dr. Khalid Aliyu yayi kira ga limamai d a shugabbannin addini su dage wajen yawaita addu'o'i da zummar Allah ya tona asirin dukkan wadanda suke haddasa wannan fitina.
A nasa bangaren babban jami'i a helkwatar kiritoci ta CAN Pastor Simon Dolli, ya tsame addini daga cikin dalilanda suke haddasa fitina. Yace addini tamkar makaranta ce, inda mutum mai 'yaya biyu ko wanne yake zuwa wata makaranta dabam, amma da zarar sun komo gida zasu ci gaba da zama 'yan uwa.
Ga karin bayani.