Wasu jaridun Najeriya sun ruwaito cewa a taron majalisar tsaro da za'a gudanar a aranar Labara wato gobe za'a tsayar da shawarar yiwuwar dakatar da gwamnonin jihohinsu suke cikin dokar ta baci da 'yan majalisun su. Hafsan sojojin sun zargi gwamnonin da wasu dattawan jihohin cewa su ne suke kawo cikas a yakin da sojojin keyi da kungiyar Boko Haram.
Alhaji Usman Ibrahim mai baiwa gwamnan Adamawa shawara akan lamuran zabe yace ba wani abu ba ne illa sharrin mutane kamar yadda gwamnan jihar Adamawa ya rubuta a wasikar da ya rubutawa gwamnonin arewa. Gwamnan ya nuna irin barnar da ake yi da kuma yadda ake anfani da wasu a cikin jami'an tsaro. Ire-irensu ne suke ciwa mutane zarafi da mutunci suna kuma neman raba kasar. Yace yana son su gane cewa gwamnatin yanzu ba ta soja ba ce. Ta dimokradiya ce.
Shugabannin addini ma sun fara mayarda martani dangane da batun. Wani Reverend Simeon Fajo yace Najeriya an ginata ne akan dokoki. Yace babu wata doka da tace idan shugaban kasa ya kafa dokar ta baci sai a cire gwamnonin. Yace duk wanda ya bada shawarar a yi hakan tamkar yana gini ne a iska. Yace wace doka za'a yi anfani da ita a dakatar da gwamnonin?
Duk da karewar dokar ranar 19 ga wannan watan har yanzu gwamnatin tarayya bata cire dokar ba. Akwai wata majiya da tace za'a cigaba da dokar har wata mai zuwa. To ko gwamnati nada ikon yin hakan? Barrister Solomon Dalung dan rajin kare hakin Biladama yace bayan an sabunta dokar sau daya shugaban kasa bashi da wani ikon cigaba da kafa dokar. To saidai yace gwamnatin yanzu bata bin tsarin doka. Gwamnati ce mai yin mulkin kama karya da danniya sabili da haka babu mamaki idan ta gwada yin wani abu.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.