Makasudin taron shi ne domin a tattauna matsalar tsaro a yankin arewacin Najeriya. Wannan matakin da kungiyar gwamnonin ta dauka ya biyo bayan wata wasika ne da gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako ya rubutawa gwamnonin inda yake gargadin gwamnonin da su tashi tsaye domin wani shirin da ya kira na karar da yakin arewa.
Alhaji Danladi Ndayabo kakakin shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Neja Dr Muazu Babangida Aliyu yayi karin haske akan taron da zasu yi tare da makiyayan. Yace wasu na ganin kashe kashe da ake yi a wasu sassan kasar ba makiyaya ba ne da manoma. Dalili ke nan da gwamnonin suka kira taron suka kuma bukaci kungiyar Miyatti Allah ta kasance wurin domin a duba a gano hanyoyin da za'a wanzar da zaman lafiya da kuma kawo karuwar arziki a arewa.
Taron ya zo daidai lokacin da zubar da jini a arewa ya kai intaha lamarin dake bukatar magancewa ko ta halin kaka.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.